Tsoffin Naira: Sace-sacenku Ya Tashi a Banza, Kwankwaso Ya Caccaki Gwamnonin APC Kan Sukar Buhari

Tsoffin Naira: Sace-sacenku Ya Tashi a Banza, Kwankwaso Ya Caccaki Gwamnonin APC Kan Sukar Buhari

  • Sanata Rabiu Kwankwaso ya caccaki gwamnonin APC kan sukar Shugaba Muhammadu Buhari kan sauya kudi
  • Dan takarar shugaban kasa na NNPP ya ce bai san abu za su kai ga har gwamnoni za su fara zagin shugaban kasar ba
  • Kwankwaso ya ce biliyoyin naira da suka sata suka boye a gida ya zama mara amfani a yanzu da wannan matakin

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, ya yi wa gwamonin jam'iyyar APC wankin babban bargo kan sukar Shugaban kasa Muhammadu Buharia saboda sauya kudi, Daily Trust ta rahoto.

Babban bankin Najeriya (CBN) wanda ya fito da sabon kudi a shekarar bara ya ayyana 31 ga watan Janairu a matsayin ranar daina amfani da tsoffin N200, N500 da N1000.

Kwankwaso
Tsoffin Naira: Sace-sacenku Ya Tashi a Banza, Kwankwaso Ya Caccaki Gwamnonin APC Kan Sukar Buhari Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Hakan ya haifar da zazzafan takaddama. Bayan matsin lamba daga bangarori daban-daban, babban bankin ya dage wa'adin da kwanaki 10.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari Ya Zolaye Ganduje: Ka Tafi Ka Kai Tsaffin Nairan Ka CBN Idan Na Halas Ne

Wasu gwamnonin jam'iyya mai mulki sun nemi shugaban kasa ya shiga lamarin, inda ya nemi su ba shi kwanaki bakwai ya dauki mataki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai kuma bayan kwanaki uku da ganawarsu da Buhari, gwamnonin APC uku sun shigar da kara don kalubalantar batun sauya kudin a babban kotun koli.

Kotun ta umurci CBN da kada ya aiwatar da wa'adin amma Godwin Emefiele, gwamnan na CBN, ya ce babu gudu babu ja da baya.

Buhari ya dan ba hukuncin kotun hadin kai a kaikaice inda ya yi umurnin kara wa'adin N200 sannan ya ayyana cewa tsoffin N500 da N1000 ba halastattu bane kuma a kasar.

Hakan ya haddasa hargits a fadin kasar. Gwamnonin jam'iyyar mai mulki sun bi sahun masu caccakar Buhari kan lamarin.

Yayin da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi zargin cewa manufar sauya kudi shine don kawo tsaico ga damokradiyyar Najeriya, takwaransa na jihar Kaduna, Nasir El-Rugfai ya bukaci mazauna jihar su yi watsi da umurnin Buhari.

Kara karanta wannan

Bayan Jawabin Buhari, CBN Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Yan Najeriya, Ya Faɗi Abu 3 Kan Sabbin Naira

Gwamna Dapo Abiodun (Ogun), Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Abubakar Badaru (Jigawa suna cikin wadanda suka ayyana cewa har yanzu tsofgfin kudi na N500 da N1000 halastattu a jihohinsu.

Martanin Kwankwaso kan matsayin gwamnonin APC

Da yake martani kan lamarin, Kwankwaso ya ce ya kadu cewa gwamnonin APC za su iya aikata abu haka, rahoton BBC Hausa.

Ya ce:

"A kowace jiha, ana da rassan bankuna kuma a wasu jihohin, ana ma da hedkwatar kwadannan bankuna na kasa, a daya bangaren su (gwamnoni) za su kai dukkanin biliyoyin daga gidan gwamnati da sauransu.
"Amma mun gano wadannan gwamnonin suna cin zarafin shugabanninsu, suna zaginsu, na yi mamaki. Ban taba tunanin wasun su za su iya zagin Buhari har zuwa nan ba.
"A daya bangaren na yi mamakin cewa gaskiya sun fara bayyana kuma mun fara mamakin menene matsalarsu? Watakila EFCC ta yi gaskiya cewa wasu gwamnoni na boye bniliyoyin naira a gidajensu a fadin kasar.

Kara karanta wannan

"Ka Bani Mamaki" Gwamna Wike Ya Maida Martani Ga Jawabin Shugaba Buhari Kan Karancin Naira

"Yanzu manufar ya sa kudaden da suka sace ya zama mara amfani, ina ganin wannan ne dalilin da yasa suka fusata. Don haka muna farin ciki da gwamnatin tarayya kan wannan, kudaden da suka karba ya zama babu komai, ya tashi aiki."

Atiku zai sha mamaki a arewa maso gabas, APC

A gefe guda, jam'iyyar APC ta ce dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu zai shayar da Atiku Abubakar mamaki a gaben shugaban kasar gobe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng