A karshe G-5 Sun Rabu 2, 2 Sun Lamuncewa Tinubu, Gwamnonin Ibo Sun Tsayar da Atiku, Ortom Na Yin Obi

A karshe G-5 Sun Rabu 2, 2 Sun Lamuncewa Tinubu, Gwamnonin Ibo Sun Tsayar da Atiku, Ortom Na Yin Obi

  • A karshe fusatattun gwamnonin PDP biyar sun bayyana matsayinsu gabannin zaben shugaban kasa
  • Gwamnonin sun dauki bangarori daban-daban daidai da ra’ayin siyasarsu bayan takarar kasa baki daya
  • Yan kwanaki kafin zaben shugaban kasa, gwamnonin sun lamuncewa yan takarar shugaban kasa daban-daban bayan sun kasa cimma matsaya daya

Abuja - Wani rahoton Vanguard ya nuna cewa gwamonin G-5 karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun lamuncewa yan takarar shugaban kasa daban-daban bayan sun gaza cimma matsaya daya kan wanda za su goyawa baya.

Kungiyar wanda Gwamna Nyesom Wike ke jagoranta sun bayyana yiwuwar marawa dan takarar shugaban kasa daya baya ga Atiku Abubakar idan har shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyiorchia Ayu ya ci gaba da zama a kujerarsa.

Gwamnonin G-5
A karshe G-5 Sun Rabu 2, 2 Sun Lamuncewa Tinubu, Gwamnonin Ibo Sun Tsayar da Atiku, Ortom Na Yin Obi Hoto: Benue state government
Asali: Twitter

Sun sha nana ta cewa kundin tsarin mulkin PDP ya sanar da cewar a raba mukaman jam’iyyar a tsakanin yankunan arewa da kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan Wike, Bola Tinubu Ya Lallaɓa Wurin Wani Gwamnan PDP Ana Dab da Zaɓen 2023

Bayan sun gano cewa yan takarar da suke ra’ayi na iya kawo cigaba ko cikas ga makokar siyasarsu, sai gwamnonin suka zabi yin yan takarar da suke ganin za su karfafa damammakinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Baya ga Wike wanda baya neman takarar kowace kujera, sauran takwarorinsa hudu suna kan takardar zabe.

Yayin da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ke neman zarcewa, Samuel Ortom na Benue, Okezie Ikpeazu na Abia da Ifeanyi Unguanyi na Enugu suna takarar kujerar sanatoci.

Ana rade-radin Wike da Makinde sun nuna goyon bayansu ga takarar Bola Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Ortom bai boye goyon bayansa ya Peter Obi ba kuma fito fili ya lamuncewa dan takarar na Labour Party.

Wani babban dan jam’iyyar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce Ikpeazu da Ugwuanyi suna goyon bayan Atiku.

Kara karanta wannan

Jemage: Bani Maka Kamfen, Ba Kuma Na Hamayya Da Kai, Wike Ga Bola Tinubu

Ya ce:

“Zan iya fada maku, daga Ugwuanyi har Ikpeazu sun yarda za su marawa Atiku baya don lashe zabe a jihohinsu.”

Kwanaki bakwai kafin zabe, G-5 basu tsayar da dan takarar shugaban kada ba

Haka kuma, jaridar Punch ta rahoto cewa kasa da maki guda kafin zaben, gwamnonin G-5 sun gaza tsayar da dan takarar shugaban kasa.

A cewar rahoton, kudirin gwamnonin yasa sun gaza cimma matsala ya kan wanda za su zaba a matsayin kungiya.

Tinubu ya yi wa mutanen Borno halacci, Zulum

A wani labarin, Gwamna Babagana zulum na jihar Borno ya jinjinawa Bola Tinubu cewa ya tsayawa jiharsu lokacin da Boko Haram ke tashe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng