Arewa Maso Gabas Zata Girgiza Atiku a Zaɓe Mai Zuwa, Jigon APC
- Babban jigon APC na ƙasa ya ce Atiku Abubakar zai sha mamaki a arewa maso gabas ranar zaɓe mai zuwa
- Mataimakin mai magana da yawun APC na ƙasa, Murtala Ajaka, yace Ralin APC na Borno kaɗai ya isa misali
- A cewarsa babu wata wahalar karancin naira da zata hana jama'ar Borno da arewa maso gabas zaɓen APC
Abuja - Mataimakin kakakin jam'iyyar APC na ƙasa, Murtala Ajaka, ya bayyana yakininsa cewa duk da wahalhalun da sauya fasalin naira ya jefa yan Najeriya, mutanen Barno da arewa maso gabas suna tare da Tinubu.
Jaridar Punch ta rahoto Ajaka na cewa duk wannan kuncin, Borno da arewa maso gabas zasu zabi ɗan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, a zaɓen 2023.
Mista Ajaka ya ce nasarar ralin kamfen Tinubu, inda aka ga dubun-dubatar mutane sun fito kwankwau da kwarkwata domin Tinubu kaɗai alama ce mai gamsarwa.
Kalaman babban jigon jam'iyya mai mulkin na zuwa ne mako ɗaya kacal gabanin zaɓen shugaban ƙasa wanda INEC ta tsara gudanarwa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tinubu zai fafata da manyan abokan hamayyarsa, Atiku Abubakar na PDP, Rabiu Kwankwaso na NNPP, da Peter Obi na jam'iyyar Labour Party.
Amma mataimakin kakakin APC ya yi ikirarin cewa babu ɗaya daga cikin manyan yan takarar shugaban kasan da zai iya gogayya da tsohon gwamnan jihar Legas.
APC zaka kiɗima Atiku a arewa maso gabas - Ajaka
A wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar da yamma a Abuja, Murtala Ajaka, ya ce jam'iyya mai mulki zata girgiza Atiku har a arewa maso gabas inda yake tutiya daga nan ya fito.
A cewarsa, babu wata wahalar karancin naira da zata dakatar da mutanen jihar Borno da baki ɗaya arewa maso gabas fitowa rumfunan zaɓe su kaɗa wa APC kuri'unsu, rahoton Leadership ya tabbatar.
A kalamansa ya ce:
"Cikar kwarin da mutane suka yi a Borno saƙo ne kai tsaye ga PDP da ɗan takararta na shugaban kasa cewa akwai babban abun mamakin dake jiransu nan gaba."
"Mutanen Barno sun yi magana da babbar murya a fili cewa suna tare da Tinubu kuma babu wahalar da zata hana su fitowa mako mai zuwa su zabi APC da ɗansu, Kashim Shettima."
Wannan Lokacinku Ne Ku Samar da Shugaban Kasa, Atiku Ga Mutanen Adamawa
A wani labarin kuma Atiku ya karkare kamfen PDP, ya lisaafa muhimman abubuwan da zai sa a gaba idan ya ci zaɓe
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya tabbatrawa yan Najeriya ba zai basu kunya ba idan suka sahale masa a hau karagar mulki.
Asali: Legit.ng