Kano: Dan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar Labour Ya Tabbatar Ta Gana Da Tinubu, Ya Yi Gum Kan Batun Sauya Sheka
- Bashir Ishaq Bashir, dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar LP ya tabbatar cewa ya gana da Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC
- Amma, Bashir bai bayyana cewa zai fita daga LP ba a halin yanzu kamar yadda aka rika hasashe a intanet, ya ce zai yi magana a gaba
- Wata majiya na kusa da Bashir ta tabbatar shi da wasu za su koma APC, hakazalika, ciyaman na LP a Kano shima ya yi ikirarin wasu na shirin barin jam'iyyarsu amma bai ambaci sunan ba
Jihar Kano - Dan takarar gwamnan na jam'iyyar Labour a Jihar Kano, Bashir Ishaq Bashir, ya tabbatar cewa ya tattauna da dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Bola Tinubu a ranar Asabar.
Hotunan dan takarar gwamnan na LP sun rika yawo a intanet a ranar Lahadi, da zargin cewa ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, ya yi watsi da takararsa na gwamna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma da ya ke magana da wakilin Daily Trust a jiya, Bashir ya tabbatar cewa ya gana da Tinubu, amma ya ce nan gaba zai fitar da sanarwa a hukumance kan matakinsa na gaba.
Na kusa da Bashir ya ce ya kammala shirin komawa APC
Amma, daya cikin na kusa da shi, wanda ya bukaci a boye sunansa ya fada wa Daily Trust cewa shi da sauran shugabannin jam'iyyar sun gama shirin komawa APC, amma banda manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar.
Bashir bai halar kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsa ba, Peter Obi a lokacin da ya ziyarci Jihar Kano.
Ciyaman din LP a Kano ya yi ikirarin wasu mambobinsu na shirin sauya sheka
A jiya, Ciyaman din jam'iyyar Labour a Kano, Mohammed Abdullahi ya ce har yanzu jam'iyyar na goyon bayan takarar Obi-Datti.
Duk da cewa ciyaman din bai kama sunan Bashir ba, ya yi zargin wasu ne shirin fita daga jam'iyyarsu, amma ra'ayin kansu ne kuma hakan bai shafi shugabannin jam'iyyar ba.
A wani rahoton kun ji cewa Yusuf Lasun, dan takarar gwamna na jam'iyyar Labour a jihar Osun ya fita daga jam'iyyar ya koma PDP.
Ademola Adeleke, gwamnan jihar Osun ya sanar da hakan yayin ralli na dan takarar shugaban kasa a Osogbo.
Asali: Legit.ng