Zaben Shugaban Kasa: Bamu Goyon Bayan Kowane Dan Takara, Amurka

Zaben Shugaban Kasa: Bamu Goyon Bayan Kowane Dan Takara, Amurka

  • Amurka ta bayyana cewa ba bu ɗan takarar da take goyon baya a zaɓen shugaban Najeriya da za'a gudanar nan da 'yan kwanaki
  • Molly Phee, ce ta bayyana haka yayin da ta jagoranci tawagar wakilan gwamnatin US suka kai ziyara hedkwatar INEC
  • Farfesa Mahmud Yakubu ya sake jaddada cewa INEC ba jam'iyyar siyasa bace kuma ba ta tare da kowane ɗan takara

Abuja - Gwamnatin ƙasar Amurka ta jaddada cewa bata goyon bayan kowane ɗan takara a zaben shugaban Najeriya wanda zai gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Rahoton jaridar Daily Trust ya ce mataimakiyar Sakataren hukumar kula da harkokin ƙasashen nahiyar Afirka ta Amurka, Molly Phee, ce ta faɗi haka jiya a Abuja.

Manyan yan takarar shugaban kasa.
Zaben Shugaban Kasa: Bamu Goyon Bayan Kowane Dan Takara, Amurka Hoto: Peter Obi, Tinubu
Asali: Facebook

Phee ta bayyana matsayar Amurka ne yayin da ta jagoranci wakilan ƙasar haɗi da Jakadan Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard, zuwa ziyara hedkwatar hukumar zaɓe INEC.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: "Tsoffin Takardun Naira Sun Daina Amfani" CBN Ya Fitar da Sabon Jawabi

Molly Phee ta ce, "Ina kara bayani a fili cewa gwamnatin ƙasar Amurka ba ta goyon bayan kowane ɗan takara ko jam'iyya. Muna bayan shirya zaɓe, muna bayan Demokaradiyya."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da take bayanin cewa Amurka na girmama kawancenta da Najeriya, ta ce:

"Muna da banbancin tsarin mulkin Dimukuraɗiyya kuma muna karfafa hanyar ganin an shirya zaɓe sahihi kuma ingantacce. Ina farin cikin cewa muna da kwarin guiwa zaku gama zaɓe cikin nasara."
"Tun 1999 Najeriya ke rainon gina mulkin Dimukuradiyya kuma yanzu, INEC karkashin Ciyaman ɗinta da tallafin tawagarsa, yan Najeriya sun samu natsuwa za'a yi gaskiya a zaɓe na gaba."

INEC ba jam'iyya bace - Yakubu

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta, Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce INEC ta maida hankali kan shirya zaɓe, kamar yadda This Day ta ruwaito.

"Kamar Amurka, INEC ta maida hankali kacokan kan shirya zaɓe, INEC ba jam'iyyar siyasa bace, bamu da ɗan takara ko ɗaya a zaɓe mai zuwa," inji shi.

Kara karanta wannan

INEC Na Goyon Bayan Wani Ɗan Takara Ko Jam'iyya a 2023? Mahmud Yakubu Ya Tsage Gaskiya

Jam'iyyar PDP Ta Soke Gangamin Kamfen Atiku a Ribas

A wani labarin kuma Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya soke ralin kamfe a jihar Ribas

Yayin zantawa da manema labarai a Patakwal, shugaban PCC-PCC na Ribas ya bayyana cewa sun dauki wannan matakin ne saboda dalilai masu alaƙa da tsaro.

A cewarsa duba da yadda abubuwa suka cakude a siyasar Ribas, Atiku ya faɗa mana ba zai so a zubda jinin mutane saboda ralinsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262