Babu Wani Gwamnan Arewa Na APC Da Zai Tabuka Wa Tinubu Abin Kirki a Zaben Bana, Inji Tsohon Shugaban NHIS
- Tsohon shugaban hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf ya magantu kan zaben 2023
- Farfesa Yusuf ya yi hasashen cewa babu gwamnan arewa da zai iya kawowa Asiwaju Bola Tinubu jiharsa a zabe mai zuwa
- Saura kwanaki 12 a gudanar da babban zaben shugaban kasa na bana
Tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta Najeriya (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya yi hasashe kan yadda babban zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu za ta kasance a bangaren jam'iyyar All Progressives Congress (APC)
Farfesa Yusuf ya bayyana cewa babu wani daga cikin gwamnonin APC a Arewa da zai iya kawowa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu jiharsa a zabe mai zuwa.
Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 13 ga watan Fabrairu, lokacin da ya bayyana a wani shiri na Channels TV kan zaben 2023.
Tsohon shugaban na NHIS ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Babu daya daga cikin gwamnonin APC a Arewa, da ke da yardar jama'a da har zai iya kawo jiharsa ga shi (Tinubu)..Babu."
A cewarsa, siyasar Tinubu na yanki ne musamman a Lagas inda ya ce babu kamarsa, babu mai kalubalantarsa.
Farfesa Yusuf ya kara da cewar koda dai dan takarar na APC ya gina mutane, har yanzu bai da gogewa a siyasa a matakin kasa baki baya.
Ya kara da cewar a arewa, Tinubu baya magana da mutane, yana mai ikirarin cewa dan takarar shugaban kasar na APC yana bayar da kwangilar kamfen din ne kawai ga mawaka da gwamnonin APC.
Ya ce:
"Idan aka zo bangaren kamfen, yana rawa ne kawai sannan sai ya tafi."
Mafarkin Buhari na son mika mulki ga dan takarar APC zai yi wuya ya zama gaskiya
Da yake magana a kan muradin shugaban kasa Muhammadu Buhari na son mika mulki ga dan takarar APC, tsohon shugaban na NHIS ya ce burin mutane ne kadai zai yi tasiri.
A ra'ayinsa, ya ce Buhari ya dakushe duk wani tasiri da kyakkyawan nufin da yake da shi a gida da wajen kasar kuma cewa saboda haka burinsa na mika mulki ga dan takarar APC ba zai zama gaskiya ba, rahoton Punch.
Jam'iyyar LP a kudu maso yamma ta yi maja a cikin APC
A wani labarin kuma, jam'iyyar Labour Party ta rushe gaba daya tsarinta a yankin kudu maso yamma inda suka yi maja a cikin jam'iyyar APC mai mulki.
Asali: Legit.ng