Tikitin Musulmi Da Musulmi: Fani-Kayode Ya Bayyana Abin Da Zai Faru Da Kiristoci Idan Obi Ya Fadi Zabe

Tikitin Musulmi Da Musulmi: Fani-Kayode Ya Bayyana Abin Da Zai Faru Da Kiristoci Idan Obi Ya Fadi Zabe

  • Jigon jam'iyyar APC mai mulki a kasa, Femi Fani-Kayode, ya mayar da martani ga Pa Ayo Adebanjo, shugaban Afenifere a baya-bayan nan
  • Tsohon ministan sufurin jiragen saman ya ce bai yarda da abin da Adebanjo ya fada ba na cewa Idan Obi ya sha kaye, ta yi wu kirista daga kudu ba zai taba shugabancin Najeriya ba a gaba
  • Fani-Kayode, a cikin wani rubutu da ya yi a Twitter a ranar Alhamis, 9 ga watan Fabrairu, ya ce Kiristoci daga Arewa da Kudu da musulmi daga arewa duk za su shugabanci Najeriya a gaba

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode, ya yi martani kan ra'ayin shugaban kungiyar Afenifere, Pa Ayo Adebanjo, dangane da nasarar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour a zaben 2023.

Pa Adebanjo ya ce yan Najeriya su shirya ganin rikici bayan zabe idan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi, bai ci zaben da ke tafe ba.

Kara karanta wannan

Wani Ya Shiga Katuwar Matsala a kan Zargin ‘Danuwan Buhari da Ganin Bayan Tinubu

FFK da Obi
Tikitin Musulmi Da Musulmi: Fani-Kayode Ya Bayyana Abin Da Zai Faru Da Kiristoci Idan Obi Ya Fadi Zabe. Hoto: Mr Peter Obi, Femi Fani-Kayode
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Fani Kayode ya yi martani

Da ya ke martani kan maganan, jigon na jam'iyyar All Progressives Congress, Femi Fani-Kayode ya tafi shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 9 ga watan Fabrairu, don yi wa shugaban Afenifere gyara.

Rubutun da ya yi a Twitter wanda Legit.ng ta gani a ranar Juma'a, 10 ga watan Fabrairu ya ce:

"Idan Obi bai ci zabe ba zai yi wuya wani kirista daga kudu ya zama shugaban Najeriya a gaba" - Baba Ayo Adebanjo.
"Baba na, wannan ba gaskiya bane.
"Kirista daga kudu da Kirista daga Arewa da Musulmin arewa duk za su shugabanci kasar mu a gaba.
"Mu al'umma daya ce."

Yan Najeriya sunyi martani

Wasu yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu a shafin Twitter na Fani Kayode.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: APC Ta Dage Taron Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa A Kano

@AdamAbbaAji ya ce:

"Na gode bisa wannan sakon mai gamsarwa!!! Dole mu hada kai mu dena biye wa masu son raba kanmu da addini ko yanki."

@Mazi_Emeke ya rubuta:

"Idan wannan tikitin na muslmi da musulmi ya yi nasara, Kirista ba zai sake mulkar Najeriya ba.
"Jam'iyyun siyasa za su ce idan muka tsayar da kirista, za mu fadi zabe.
"Dole a ki amincewa da shi."

"Zabi Peter Obi."

@J_mknite ya rubuta:

"Tikitin addini daya ba zai taba yin nasara ba a Najeriya.... Ranar da hakan ya faru shine farkon rushewar Najeriya."

@echomaestro5 ya rubuta:

"Kuma ka yarda da kanka?"

Fani-Kayode: Da 'Aladu' Na Ke Tare A Lokacin Da Na Soki Bola Tinubu

Femi Fani-Kayode, direktan karamar kwamitin watsa labarai na kamfen din Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC ya bawa masu zarginsa da sukar dan takarar shugaban kasar na APC amsa.

Tsohon ministan sufurin ya ce a lokacin da ya rika sukar Tinubu yana tare da 'Aladu' ne.

Kara karanta wannan

Takarar Shugaban Kasa: Mai Goyon Bayan Atiku, Reno Omokri Ya Soki Peter Obi, Ya Yaba Wa Bola Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel