2023: Dama Daya Tal Peter Obi Ke Da Ita Ya Hada Kai NNPP, Kwankwaso

2023: Dama Daya Tal Peter Obi Ke Da Ita Ya Hada Kai NNPP, Kwankwaso

  • Tsohon gwamnan Kano ya bayyana damar Peter Obi ta samun nasara a zaben shugaban kasa 2023
  • Ɗan takarar shugagan kasa na NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya ce Obi zai samu nasara ne idan ya haɗa kai da shi
  • Kwankwaso ya kuma maida martani kan zabukan gwajin da ake shiryawa a kafafen sada zumunta

Mai neman zama shugaban kasa karkashin inuwar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya ce dama ɗaya ta rage wa takwaransa na Labour Party, Peter Obi, idan har yana son samun nasara a zaɓen 2023.

Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano ya ce maja da NNPP ce kaɗai damar Peter Obi na zama cikin tawagar da zasu samu nasara a zaben 25 ga watan Fabrairu.

Rabiu Musa Kwankwaso.
2023: Dama Daya Tal Peter Obi Ke Da Ita Ya Hada Kai NNPP, Kwankwaso Hoto: KwankwasoRM
Asali: Twitter

Ɗan takarar NNPP ya yi wannan furucin ne yayin hira da kafar talabijin ɗin Channels tv a shirinsu na musamman kan zabe 'The 2023 Verdict' ranar Jumu'a da yamma.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Fadi Abin da Zai Iya Jawo Barkewar Rigima a Sakamakon Zaben 2023

Da aka tambaye shi kan damar Obi duba da yadda ɗan takarar shugaban kasa na LP ke jan ragama a zaɓen gwajin da ake shiryawa, Kwankwaso ya ce damar Obi ta dogara ne idan ya haɗa kai da shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa, ya ce:

"Bari na kara maimaita maku abinda na faɗa a nan wurin lokacin muna shirin cure wa wuri guda, dama ɗaya da suke da ita (LP) ta dogara da mu idan muka yi maja."

Punch tace da yake martani kan zabukan gwajin da aka gudanar a Intanet, Kwankwaso ya nuna mamakin ta ya na farko zai ba shi kaso 6% na kuri'un arewa maso yamma.

Tsohon gwamnan ya ce, "Ko mahaukacin mutum ya san cewa na fi karfin kaso 06% ko Kaso 60 cikin ɗari ma na wuce nan," a yankin arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Sa Labule da Bola Tinubu a Villa, Bayanai Sun Fito

Kwankwaso ya ƙara da cewa, "Mun ga irin waɗannan alƙaluman na cikin gida a APC da PDP, kuma sun sha alwashin ba zasu fallasa ba," A cewarsa yana jin daɗin yadda wasu ke kallonsa karamin kwaro.

PDP ta sauya ranar zaben fidda gwani a jihohi 3

A wani labarin kuma Jami'Iyyar PDP Ta Zabi Sabuwar Ranar Zaben Fidda Dan Takarar Gwamna a Jihohi Uku

Sakataren tsare-tsare na PDP ta ƙasa ta fitar da sanarwan sauyin da aka samu a harkokin zaɓen fidda ɗan takarar gwamna na jihohin Imo, Bayelsa da Kogi.

Jam'iyyar PDP ta ce an samu sauyin ne sakamakon yanayin kakar kamfen da ake ciki gabanin babban zaben wannan shekarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262