Shugaba Buhari da Tinubu Sun Shiga Ganawar Sirri a Aso Villa
- Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, da Bola Tinubu, sun shiga ganawar sirri a Aso Villa da daren ranar Jumu'a
- Duk da babu sahihan bayanai kan abinda zasu tattauna, an ce ganawar ba zata rasa alaƙa da kulla dabarun babban zabe mai zuwa ba
- Karo na farko kenan da manyan jiga-jigan APC mai mulki zasu gana bayan ralin kamfen da ya gudana a Sakkwato
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya shiga ganawar sirri yanzu haka da ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock.
Tinubu, wanda ya hakura da liyafar girmamawan da aka shirya dominsa a babban ɗakin taron ƙasa da ƙasa dake Abuja, ya sanar da cewa yana da zama da Buhari da karfe 9:45 na dare.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa yayin da yake ba da uzurinsa, Bola Tinubu ya ce:
"Ina da zama mai girma, jiya da dare shugaban ƙasa ya kira ni ya nemi na je na same shi a gida da karfe 9:45 na daren nan (Jumu'a). Me kuke tsammanin zan yi, na ki zuwa na saba wa umarninsa?"
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ku sani umarni ne daga sama, ka same ni da karfe 9:45 na dare. Ba zan yi watsi da wannan liyafa ba ko na rage mata armashi, ya kamata na zo na fahimtar da ku halin da ake ciki."
"Wannan ya sa akwai abokin gami a tseren kujera irin wannan, ina da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa (zai wakilce ni)."
Me Buhari da Tinubu zasu tattauna?
Duk da ba'a bayyana batutuwan da taron jiga-jigan biyu zai maida hankali ba, amma wata majiya tace ganawar ba zata rasa nasaba da kulle-kulle da dabarun tunkarar zaɓe ba.
Majiyar ta ce ganawar jagororin jam'iyya mai mulkin ba zai rasa alaƙa da shiri da lalubo dabarun tunkarar zaɓen shugaban kasa ba wanda zai gudana nan da mako biyu.
Wannan shi ne karo na farko da Tinubu zai gana da shugaban kasa bayan ya jaddada cikakken goyon bayansa ga ɗan takarar a ralin APC na jihar Sakkwato ranar Alhamis.
Har yanzu da muke haɗa wannan rahoton, shugaban kasa da Tinubu na tare sun tattaunawa a gidan gwamnatin tarayya, kamar yadda Dailypost ta ruwaito
Gwamnan Gombe ya rasa hadiminsa
A wani labarin kuma Hadimin Gwamna Yahaya Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar APC Zuwa NNPP
SA na gwamnan jihar Gombe, Chokalin Waja, ya rubuta wasikar aje aiki kana ya sauya sheka daga APC mai mulki zuwa NNPP mai kayan marmari.
A cewarsa, bai ga amfanin muƙamin da aka naɗa shi ba saboda ba ya aiki kuma ba'a karban shawarin da yake baiwa gwamnati.
Asali: Legit.ng