Dalilin Da Yasa Peter Obi Zai Samu Kuri'u da Yawa a Arewa a Zaben 2023
- Wani jigon jam'iyyar LP ya bayyana manyan dalilan da zasu ja hankalin 'yan arewa su jefa wa Peter Obi kuri'unsu
- Ibrahim Abdulkarim, ya yi hasahen cewa ɗan takarar LP zai samu tulin kuri'u a arewa fiye da kudancin Najeriya
- Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra na ɗaya daga cikin manyan 'yan takara uku da ake ganin zasu iya kai bantensu a zabe mai zuwa
Jigon Labour Party (LP), Ibrahim Abdulkarim, ya ce mai neman zama shugaban kasa na jam'iyyarsa, Peter Obi, zai samu kuri'u da yawa a arewa fiye da wadanda zai samu a kudu a zabe mai zuwa.
Mista Abdulkareem ya ce 'yan arewa zasu zaɓi Obi ne saboda sun fusata kuma sun gaji da rashin tsaro, rashin ilimi, zaman kashe wando da sauran matsaloli da suka addabi yankinsu.
Ɗan siyasan ya yi wannan hasashen ne ranar Laraba a cikin shirin gidan Talabijin Channels TV na musamman kan zaɓe 'The 2023 Verdict.'
Ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Bari na faɗa maku abinda ke faruwa a arewa, da yawan mutane na ganin Peter Obi ba zai samu komai ba daga kuri'un 'yan arewa."
"Da ikon Allah Obi zai samu damin kuri'u daga arewa, mai yuwuwa ma su zarce kuri'un da zai samu daga kudu saboda mutanen arewa sun fi harzuƙa fiye da 'yan kudu."
Abdulkareem, daraktan kwamitin kamfe mai zaman kansa, ya ce ya gudanar da bincike kuma sakamakon ya nuna yan arewa na son Obi/Datti saboda sun fusata da yadda 'yan siyasa suka maida yankinsu.
"Makon da ya shige na je Kano, a gidajen Radiyo uku na ba da damar kiran waya, tsawon mintuna 45 duk wanda ya kira yana goyon bayan maganata kuma sun amince da manufofin LP."
"Sun nuna gamsuwa da tunaninmu da akidar da muka zo da ita. Ba yin kanmu bane addu'ar mutane Allah ya amsa."
A cewar Abdulkarim, yan arewa mazauna kauyuka sun gaji da wahalhalu kuma sun ƙagu a samu canji a shugabancin kasar nan, vanguard ta rahoto.
Gwamna Umahi Ya Ayyana Goyon Baya Ga Buhari Game da Canja Naira
A wani labarin kuma Gwamna jihar Ebonyi, mamban APC ya nuna tsantsar goyon bayansa ga shirin canja takardun naira
Gwamnan, wanda ya san komai game da matsananciyar wahalar da mutane ke sha, ya ce yana yakinin Buhari zai share hawayen yan Najeriya.
Tun bayan bullo da wannan tsarin, babban banki da bankunan kasuwanci ke musayar yawu kan wanda ke da laifin jefa mutane cikin wahala.
Asali: Legit.ng