Canjin Kudi: Makiya Dimokradiyya Ne Ke Son Kawo Rudani A Najeriya, In Ji Tinubu

Canjin Kudi: Makiya Dimokradiyya Ne Ke Son Kawo Rudani A Najeriya, In Ji Tinubu

  • Tinubu ya bayyana cewa halin da ake ciki na karancin kudi da man fetur wasu marasa son cigaba ne suka janyo
  • Dan takarar shugabancin kasar na APC ya roki mutane da su kwantar da hankali su kuma guji fitina har zuwa lokacin da za a shawo kan lamarin
  • Tsohon gwamnan na Jihar Lagos ya bayyana cewa da ake ciki an kirkiri hakan ne da gangan don kawo cikas ga shirin babban zabe

Lagos - Dan takarar shugabancin kasa a inuwar jam'iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu, ya ce makiyan dimukradiyyar Najeriya ne su ke so kawo rudani ta hanyar amfani da karancin man fetur da kuma takardin Naira a babban zabe mai zuw, rahoton Punch.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da dan takarar ya ke rokon yan Najeriya da su kwantar da hankalin su kan karancin takurdun kudi da kuma man fetur da ya jefa kasar nan mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

"Nima Ina Ji A Jiki Na", Minista Mai Karfi A Gwamnatin Buhari Ya Ce Shi Kansa Ba Shi Da Sabbin Takardun Naira

Bola Tinubu
Canjin Kudi: Makiya Dimokradiyya Ne Ke Son Kawo Rudani, Tinubu. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohon gwamnan na Jihar Lagos, wanda yayi batun a Abuja ranar Talata, ya ce abin da ''makiyan dimukradiyya" ke son cimmawa, suna so su sanya fada da tashin hankalin da zai kawowa zabe tsaiko.

Da gangan aka jefa al'umma cikin wahala, Tinubu

A wata sanarwa da direktan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben APC, Bayo Onanuga, Tinubu ya ce da gangan aka jefa mutane cikin rashin kudi da kuma wahalar mai da nufin jefa talaka cikin kunci da bacin rai.

A cewar Tinubu:

''Wannan lokaci ne mai tsauri a tarihin kasar mu yayin da aka tilasta mutane bin dogayen layuka tsahon awanni don shan mai a ababen hawa ko kuma don cirar kudaden su a bankuna.
''Ina jajantawa yan Najeriya gaba daya musumman talakawa da suke cikin kunci da radadin halin da dokar babban bankin kasa da karancin mai ya janyo. Yayin da gwamnati ke cigaba da kokarin shawo kan matsalar, mu yi hakuri, mu zauna lafiya mu kuma kaurace wa duk abin da zai kawo tashin hankali ta rudani.''

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Allah Na Dogara Da Shi Domin Nasara," Tinubu Ya Fada Wa Mahalarta Taron Ruwa Da Tsaki Na APC

''Abin da masu adawa kuma mikiyan dimukradiyya su na so suyi amfani da wannan damar dan kirkirar tashin hankali da tarzomar da za ta iya dakatar da gudanar da zabe da kuma cigaba da kuntata halin rayuwa a kasarmu.''
''Dole mu nuna ba su isa ba. Dole mu kula mu kuma tsaya tsayin daka don kare dimukradiyya ta hanyar tabbatar da an gudanar da zabe lafiya kuma cikin kyakkyawan tsari."

Zaben 2023: Gwamnan Legas Ya Dakatar Da Kamfen Dinsa Har Sai Baba Ta Gani

A wani rahoton kun ji cewa Gwamna Babajide Sanwo Olu na jihar Legas ya dakatar da kamfen dinsa a dukkan sassar kasar har sai baba ta gani.

Gwamnan da jam'iyyarsa sun dauki wannan matakin ne duba da mawuyacin hali da sauyin fasalin naira da karancin man fetur ya jefa mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164