Zaben 2023: "Allah Na Dogara Da Shi Domin Nasara," Tinubu Ya Fada Wa Mahalarta Taron Ruwa Da Tsaki Na APC
- Takarar Bola Tinubu na cigaba da samun tagomashi a yayin da masu ruwa da tsaki da ke kula da neman goyon baya ga takararsa
- Kungiyar yayin bayyana cikakken goyon bayan domin ganin Tinubu ya zama shugaban Najeriya na gaba ta ce Allah ta dogara da shi domin nasara
- Kungiyar ta cigaba da cewa gwamnatin Tinubu za ta kawo cigaba tare da inganta hadin kai a kasa
FCT Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Bola Ahmed Tinubu ya ce ya dogara ga Allah ne domin yin nasara a zaben shugaban kasa na 2023 saboda "Allah ne ke bada mulki."
Wakilin Legit.ng a Abuja, Nasir Danbatta, ya rahoto cewa Asiwaju ya bayyana hakan ne a wani taro na musamman da bangaren da ke kula da harkokin da suka shafi neman goyon baya daga masu ruwa da tsaki a babban kwamitin yakin neman zabe na jam'iyyar APC ta shirya a Abuja a ranar Lahadi, 5 ga watan Fabrairun 2023.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yadda Allah zai kai Tinubu ga nasara
Tinubu ya yi bayani cewa, me imani na gaskiya a kullum neman taimakon Ubangiji yake sakawa kan gaba a dukkan lamuransa, ciki har ma da neman ofishi na siyasa.
Kana ya kuma bada shawara ga malaman addinin da kada su bar miyagun 'yan siyasa su gautar dasu wajen zaben wakilai a kakar zabe me zuwa, tare da bada tabbacin cewa jam'iyyarsa ta APC na nufin alheri ga Najeriyar da a yau ke cikin mawuyacin hali.
Tinubu ya bayyana shirinsa ga al'ummar Najeriya, ya nemi goyon baya
Tinubun dai ya jaddadawa taron shugabannin cewar zabe me zuwa dama ce da zata kara karfin jijiyoyin da suka hada 'yan Najeriya waje guda a matsayin mutanen da jajircewarsu zata haifar da da me ido wajen gina kasa.
A jawabinsa na bude taron, Malam Jamilu Haidara ya yi fadi cewa taron kira ne na musamman ga 'yan Najeriya daga sassa daban-daban na rayuwa, kama daga malaman addini daga Arewaci da kudanci.
Har wayau, ya kuma bayyana mahalarta taron a matsayin masu kishin kasa duba da irin rawar da suke takawa dangane da makomar Najeriya.
Tinubu mai fafutukar tabbatar da shugabanci nagari ne, In ji Ribadu
Shugaban bangaren da ke kula da tattaro masu ruwa da tsaki, Malam Nuhu Ribadu ya ce, Tinubu ya gina isassun ababen fada na alheri tun zamanin da yayi gwamna a Legas har zuwa yau, ya bada gudunmawa wajen karfafawa da taimakon mutane a kasa baki daya kana ya dade yana da’awar samun gwamnati ingantacciya a karkashin demokaradiyya.
Gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar a nashi jawabin a wajen taro ya jawo hankulan 'yan Najeriya da suyi la'akari da tarihin Asiwaju Bola Tinubu yayinda yayi wakilci a baya sannan su watsar da soki burutsun da yan adawa keyi akansa. Ya kuma kara da cewa, dan takarar jam’iyar tuni ya bayyana kudirorinsa da za su kawo ci gaba a kasar.
Kadan daga cikin mahalarta taron sun hada da tsohon kakakin majalisar tarayya Oladimeji Bankole, tsohon ministan babban birnin tarayya, Dr. Aliyu Modibbo, tsohon sakatare na dindindin a fadar shugaban kasa, Mal Jalalu Arabi, Mal. Nafiu Baba Ahmed, babban sakatare a majalisar koli dake karfafa tabbatar da Sharia a Najeriya, Sheik Dr. Khalid Aliyu, Babban Sakatare na Jama'atu Nasril Islam, sannan kuma mamba na kwamitin amintattu ta majalisar koli, Sheikh Dr. Bashar, Sheik Dahiru Bauchi, Sheikh Prof. Abdullahi Pakistan, Sheikh Khalid Usman Khalid, Dr. Aliyu Tilde, Sheikh Dr. Haroun Ajah, Sheikh Muhammad Sirajuddeen, babban mai bada shawara na musamman a APC, Mahmud Jega, da dai sauransu.
Kiristoci Sun Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Domin Nasarar Bola Tinubu A Zaben 2023
A yayin da zabe ke karatowa, mabiya addinin kirista a jihar Oyo sun shirya addu'a na musamman domin nasarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023.
Asali: Legit.ng