Dan Allah Ku Yafe Mun, Tinubu Zai Dora Daga Inda Na Tsaya, Buhari
- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya roki 'yan Najeriya su yi hakuri su zabi Bola Ahmed Tinubu a watan nan
- Yayin ralin APC a jihar Katsina ranar Litinin, Buhari ya ce Tinubu zai gyara kuskuren gwamnatinsa ya ɗora daga inda ya tsaya
- A 'yan makonnin nan dai siyasa ta ɗau zafi a Najeriya musamman kan batun sauya takardun kuɗi da karancin Fetur
Katsina - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya roki ɗaukacin 'yan Najeriya da su yafe wa gwamnatinsa kuma su jure wa radadin da ta kawo masu.
Buhari ya kuma tabbatar da cewa gwamnati mai zuwa ta Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC, zai gyara kura-kuran kuma ya ɗora daga inda ya tsaya.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Buhari ya yi wannan furucin ne ranar Litinin yayin da yake jawabi ga dubannin masoya da magoya baya a filin kwallon Dikko Stadium Katsina.
A wurin Ralin APC na jihar Katsina, wanda ya gudana a filin kwallon Dikko, Buhari, ya dora laifin halin da ake ciki kan faɗuwar tattalin arziki sakamakon annobar cutar Korona.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Duk da haka a cewar shugaban ƙasan, gwamnatinsa ta kawo ci gaba kuma ta samu nasarori na zamani a tsawon lokacin da ta kwashe a kan mulki.
A kalamansa, Buhari ya ce:
"Da sunan Allah, ina rokonku Dan Allah ku ƙara hakuri da mu kuma ku yafe mana. Ku faɗawa abokanku, 'yan uwa maza da mata da 'ya'yanku su ci gaba da jefa wa APC kuri'unsu."
"Ku tabbata kun zaɓi Tinubu a matsayin shugaban kasa, Dikko Raɗɗa a matsayin gwamnan jihar Katsina da sauran 'yan takarar jam'iyyar APC."
Da yake jawabi, gwamna Aminu Bello Masara ya raba yakin neman zama shugaban ƙasa gida biyu, haske bisa wakilcin Tinubu na APC da duhu watau sauran yan takara.
Tinubu ya ba da talllafin miliyan N100m
Bayan haka ya sanar da cewa Tinubu ya ba da tallafin naira miliyan N100m ga iyalai da sauran mutanen da harin 'yan ta'adda ya shafa a ƙaramar hukumar Bakori, This Day ta rahoto.
Legit.ng Hausa ta samu zantawa da ɗaya daga cikin mahalarta ralin kuma tsohon ɗan takara a APC, Usman Gide, ya ce tabbas Katsinawa sun nuna wa Buhari karar da aka sansu da ita.
Usman ya shaida wa wakilinmu cewa lokacin da Buhari ya nemi afuwa tun a wurin wasu ke cewa sun yafe masa kuma zasu zabi duk wanda ya ɗaga hannunsa.
Ya ce:
"Har yanzu Buhari na da wannan farin jinin da aka sanshi, mutane da yawa sun masa afuwa tun a wurin kamfen. APC ta shirya tsaf a Katsina da ƙasa baki ɗaya kuma mu ke da nasara insha Allah."
Sai dai wani mazaunin Katsina, Isah Mubarak, ya ce ya samu labarin shugaban kasa ya nemi a yafe masa kura-kuran da gwamnatinsa ta yi amna yana da sharadi.
A cewarsa, idan har abubuwan da ya yi da suka jefa mutane cikin wahala ba ganganci bane watakila yana da kyakkyawan niyya to zai iya yafe masa.
A wani labarin kuma Bola Tinubu ya yi karin haske game da tsamin alaƙarsa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari
Dan takarar shugaban ƙasan ya bayyana cewa duk masu ƙulle-kulle da tuggun ganin alaƙa tai tsami tsakaninsa da Buhari zasu ji kunya.
Tsohon gwamnan Legas ɗin ya kuma bayyana cewa Buhari yana bin tsarin mulkin Demokuradiyya duk da ya kasance tsohon soja.
Asali: Legit.ng