2023: Hadimin Gwamnan Sokoto Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC
- Yan kwanaki gabanin babba zaben 2023 jam'iyyar PDP ta sake shiga matsala a jihar Sokoto
- Mai ba gwamna Aminu Tambuwal shawara na musamman ya sauya sheka zuwa APC
- Abubakar Kwaire ya ce tsarin jagoranci irin na Sanata Aliyu Wamakko ne ya ja hankalinsa zuwa jam'iyyar mai mulki a kasar
Sokoto - Gabannin babban zaben 2023, Abubakar Kwaire, hadimin Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, ya sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC)
Tambuwal wanda ke wa'adinsa na biyu a matsayin gwamna shine darakta janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Atiku/Okowa. Kuma shine jagoran PDP a jihar.
A cewar wata sanarwa da Bashar Abubakar, mai ba sanata Aliyu Wamakko shawara ta musamman kan harkokin labarai, Mista Kwaire, ya samu tarba daga dan takarar gwamnan APC a jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, jaridar Premium Times ta rahoto.
Na koma APC ne saboda yanayin jagorancin sanata Wamakko, Kwaire
Sanarwar ta ce sabon dan APCn, wanda ya kasance tsohon dan majalisar dokokin jihar ya fito ne daga karamar hukumar Tambuwal ta jihar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya nakalto Mista Kwaire yana cewa ya yanke shawarar komawa APC ne saboda shugabanci mai nagarta irin na Wamakko.
Ya ce:
"Saboda haka, na yarda da Wamakko a matsayin jagoran APC da sannan idan aka zabi Aliyu don jagorantar jiharmu za a kwankwadi romon damokradiyya kamar yadda ake tsammani."
Mista Kwaire ya jaddada jajircewarsa wajen goyon bayan dukkanin yan takarar jam'iyyar zuwa ga tafarkin nasara don amfanin jihar Sokoto da Najeriya.
A jawabinsa, dan takarar gwamnan na APC ya yi wa masu sauya shekar maraba da zuwa sannan ya basu tabbacin dama da su kamar sauran mambobin jam'iyyar, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rahoto.
Kungiya ta roki yan Najeriya da su zabi Atiku a 2023
A wani labari na daban, wata kungiya mai suna 'WAZIRIN Adamawa Movement' ta ja hankalin yan Najeriya da su yi nazari da kyau kafin su kada kuri'arsu ga masu neman takarar shugaban kasa.
Kungiyar ta bukaci masu zabe da su zabi Atiku Abubakar domin shine zai iya fitar da kasar daga halin wayyo Allah da take ciki a yanzu.
Asali: Legit.ng