Zaben Shugaban Kasa Na 2023: "Da Izinin Allah, Wannan Ne Magaji Na", Buhari Ya Bude Baki Ya Magantu
- Shuguba Muhammadu Buhari ya bayyana ƙarara cewa zai cigaba da yiwa Asiwaju Bola Tinubu kamfe
- Shugaban ya bayyana wannan muhimmin kira ranar Asabar, 4 ga Fabarairu, a Lafia, Jihar Nasarawa, lokacin da yake buɗe wasu ayyuka
- Buhari ya kuma yi kira ga ýan Najeriya da su sanya cikakken kwarin gwiwa akan Tinubu su kuma kaɗa masa kuri'un su a zaɓe mai zuwa
Lafiya, Nasarawa - Shuguba Muhammadu Buhari ya yi kira ga yan Najeriya da su zabi ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Za ku iya aminta da Tinubu ku bashi kuri'a - Buhari ga yan Najeriya
Yayin ziyarar da ya kai Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa inda ya buɗe wasu muhimman ayyuka ranar Asabar, 4 ga Fabarairu, Shugaba Buhari ya tabbatar wa masu kaɗa ƙuri'a da su amince da Asiwaju a zaben 25 ga watan Fabarairu.
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa shi da tsohon gwamnan na Lagos abokai ne na sama da shekara 20 da ɗoriya, tare da bayyana cewa tare suke gwagwarmayar siyasa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da yake tabbatarwa magoya baya cewa Tinubu mai son ganin bunkasa da cigaban Najeriya ne, Shugaban ya kuma bayyana cewa da yardar Allah, jagoran APC shine zai zama shugaban Najeriya a zaɓe mai zuwa.
Zan cigaba da tallata Tinubu - Buhari
Buhari, don yin abin da aka saba, ya bayyana ƙarara cewa zai cigaba da tallata Tinubu, tare da bayyana cewa Jagaban zai bada komai nasa ga cigaban Najeriya.
Ga abinda ya ce:
"Da izinin ubangiji, Tinubu zai zama shugaban kasa yayin da nake kira ga yan Najeriya da su zaɓi ɗan takarar APC a babban zaɓe mai zuwa.
"Nasan Ahmed Bola Tinubu kamar yadda ya fada a wata magana da yayi sama da shekara 20 da suka gabata cewa babu wata ƙaramar hukuma da ban ziyarta ba daga 2003-2011 kuma na ziyarci gaba ɗaya jihohin Najeriya a 2019 lokacin da nake neman shugabanci karo na biyu kuma na karshe.
"Zan cigaba da tallafa Tinubu, yana son Najeriya kuma na tabbatar zai bada duk wata gudunmawa ga ƙasarsa da ku yan kasa."
"Ga mu da muka haɗa hannu shekara 20 da suka wuce don dawo da Najeriya hayyacinta, mu yaƙi rashawa, mu yaƙi ha'inci, mu yaƙi fatara da yunwa, muna alfahari da nasarorinka."
Asali: Legit.ng