Kano: Barazanar Kisa ta Jawo Alkali ya ce a Gaggauta Damke Shugaban Jam’iyyar APC
- Kotun tarayya ta saurari korafin da wani Bawan Allah ya shigar a kan Alhaji Abdullahi Abbas
- Mahmoud Lamido ya ce shugaban Jam’iyyar APC ya yi barazanar zai ga karshen rayuwarsa
- Alkali ya saurari Lauyan Lamido, Bashir Tudunwazirchi, sai ya bada umarni a cafko ‘Dan siyasar
Kano – A makon nan babban kotun tarayya mai zama a garin Kano, ta bada umarni ayi gaggawar cafke Shugaban jam’iyyar APC na reshen jihar Kano.
Daily Nigerian ta rahoto cewa Alkali ya amince a kama Alhaji Abdullahi Abbas ba tare da bata lokaci ba domin a bincike shi, a gurfanar da shi a kotu.
Ana zargin Abdullahi Abbas da laifin barazana ga rayuwa da kawo rashin zaman lafiya da yin wasu kalaman batanci, saboda haka aka yi kararsa.
Wani Bawan Allah, Mahmoud Lamido ya shigar da karar shugaban jam’iyyar a kotun tarayyar kasar ta hannun wani Lauyansa, Bashir Tudunwazirchi.
Yanzu-Yanzu: Murna A Yayin Da Kotu Ta Bada Hukuncin Karshe Kan Shari'ar Gwamnan PDP Mai Karfi A Babban Jihar Kudu
'Sai na batar da kai'
Jaridar ta ce Mahmoud Lamido yana ikirarin Abdullahi Abbas ya yi masa barazanar zai kashe shi ta wayar salula, inda ya fada masa ‘sai na batar da kai’.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
S.A. Amobeda mai shari’a na kotun da ke zama a garin Kano ya amince da rokon Bashir Tudunwazirchi, sannan ya daga karar sai zuwa 16 ga Fubrairu.
Sahelian Times ta ce idan an koma kotun nan da makonni biyu, Alkali zai duba ko an zartar da umarnin.
Jam'iyyar NNPP tayi farin-ciki
A wani jawabi, kakakin kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar NNPP a Kano, Sanusi Dawakin Tofa ya ce ba yau aka fara yanke irin hukuncin nan ba.
Sanusi Dawakin Tofa ya ce sau biyu a jere kenan Alkalai dabam-dabam su na tursasawa kwamishinan ‘yan sanda yin bincike a kan shugaban na APC.
Kakakin ya ce su na fata zai zama darasi ga duk ‘dan siyasar da ya rungumi rigima da kokarin kawo tashin-tashina da rashin zaman lafiya a Kano da Najeriya.
A lokuta da-dama an samu shugaban na APC mai mulki yana barazanar tade-tsaye, yana cewa ko da tsiya ko da tsiya-tsiya sai jam’iyyarsu ta lashe zabe a Kano.
Zuwan Emefele CBN a 2014
A wani rahoto da muka fitar, kun ji cewa an tona yadda Godwin Emefele ya kori na-kusa da Muhammadu Sanusi a babban bankin kasa na CBN.
Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli ya ce Emefele yana shiga ofis, ya sauke shi domin ya ba Surukinsa mukami a NSPM ba tare da bin ka’ida ba.
Asali: Legit.ng