Murna A Yayin Da Kotu Ta Bada Hukuncin Karshe Kan Shari'ar Gwamnan PDP Mai Karfi A Babban Jihar Kudu

Murna A Yayin Da Kotu Ta Bada Hukuncin Karshe Kan Shari'ar Gwamnan PDP Mai Karfi A Babban Jihar Kudu

  • A ranar Laraba, kotun koli ta yi watsi da karar da Dan Orbih na jam'iyyar PDP ya shigar na kallubalantar zaben cikin gida da ta samar da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki
  • Kotun ta bakin masu shari'a guda biyar ta yi watsi da karar da aka shigar na neman watsi da nasarar Godwin Obaseki
  • Mai shari'a Centus Nweze a hukuncin da suka yanke ya ce dole karar da aka shigar ya zama yana da tushe a hukuncin kananan kotuna kafin a duba shi

Jihar Edo - Godwin Obaseki ya yi martani kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yi kan rikicin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jihar Edo.

A ranar Laraba, 1 ga watan Fabrairu, Obaseki ya bayyana hukuncin a matsayin "Babu mai nasara, Babu wanda aka kayar" ya kuma yi kira ga mambobin jam'iyyar da mutanen Edo su hada kai da jam'iyyar da gwamnati don ceto Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Wasu Masu Son Gaje Buhari Abin Dariya Ne, Gwamnan Arewa Ya Tabo 'Yan Takarar Shugaban Kasa

Obaseki
Murna A Yayin Da Kotu Ta Bada Hukuncin Karshe Kan Shari'ar Gwamnan PDP Mai Karfi A Babban Jihar Kudu. Hoto: Governor Godwin Obaseki
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obaseki ya jinjinawa hukuncin kotun koli na baya-bayan nan

Obaseki a cikin sanarwar da ya fitar a shafinsa na Facebook da Legit.ng ta gani a ranar Laraba ya ce:

"Hukuncin kotun koli na yau, ya kawo karshen rikicin shari'a da aka dade ana yi kan yan takarar da suka samu tikiti a babban jam'iyyar mu, PDP a jihar Edo a babban zaben ranar 25 ga watan Fabrairu da ranar 11 ga watan Maris na 2023.
"A matsayin shugaban jam'iyya a jiha ta, ina kira ga kowa ya dauki wannan cigaban a matsayin nasara da zai kawo karshen rikici a jam'iyyar PDP ta Edo kuma su lura cewa nasara ce ga dukkan yan PDP. Abin da ke gaban mu yanzu shine yin nasara a babban zaben da ke tafe don wannan abin ya karfafa mu don samun nasara."

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel