Wasu Daga Cikin Masu Neman Takarar Shugaban Kasa Abun Ayi Dariya Ne, El-Rufai

Wasu Daga Cikin Masu Neman Takarar Shugaban Kasa Abun Ayi Dariya Ne, El-Rufai

  • Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa wasu yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 abun dariya ne
  • Yayin da yake bayani a iya saninsa, gwamnan ya ce aikin shugaban kasa ba abu ne da yakamata mutum dan shekara 40 da 50 ya nema ba
  • El-Rufai ya ce ya samu damar aiki da akalla shugabannin kasa 3 kuma ya fahimci wahalhalun da ke tattare da shi saboda sarkakiyar da kasar ke ciki

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana cewa wasu yan takarar shugaban kasa a babban zaben 2023 ba komai bane su face "abun dariya".

El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a shirin Sunrise Daily na Channels TV a ranar Laraba, 1 ga watan Fabrairu.

Tinubu, obi, Atiku da El-rufai
Wasu Daga Cikin Masu Neman Takarar Shugaban Kasa Abun Ayi Dariya Ne, El-Rufai Hoto: Asiwaju Bola Ahmed TInubu
Asali: Twitter

El-Rufai ya saki shekarun da bai kamata mutum ya nemi takarar shugaban kasar Najeriya ba

Kara karanta wannan

Wahalar Naira Da Mai: Akwai Wasu Na Kusa Da Buhari Da Basu Son Tinubu Yaci Zabe, El-Rufa'i

Wasu daga cikin manyan yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 sune Bola Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congres (APC), takwaransa na Peoples Democratic Party (PDP) da Peter Obi na Labour Party.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar gwamnan, zai yi matukar wahala mutumin da ke a ganiyar shekaru 40-50 ya gamsar da yan Najeriya, musamman wadanda ke harkar siyasa cewa shi ko ita suna da gogewar da za su kula da Najeriya saboda wuyan sha'ani na kasar.

Ya kara da cewa:

"Kuma wasu daga cikin mutanen da ke neman takara, magana ta gaskiya, abun dariya ne, a iya tunanina. Kowani aiki na da sauki daga nesa amma na samu damar aiki da akalla shugabannin kasa uku, kut-da-kut kuma na ga abun da aikin ke bukata da yadda yake."

El-Rufai ya kuma bayyana cewa ko kasancewa gwamna babban aiki ne amma mutane basu sani ba, sun zata abu ne mai sauki.

Kara karanta wannan

Wani hanzari: Sirri ya fito, tsohon kakakin majalisa ya ce hadari ne a ba Tinubu ragamar Najeriya

Ya ce a kodayaushe suna cewa kamata yayi ace gwamnati ta yi shi haka amma da zaran ka ce masu su zo su yi sai su fara korafi.

Ya ce:

"Kai da sun sani sun yi haka, kawo su don su yi shi, zaka fara jin labari."

Kalli bidiyon a kasa:

Na kusa da Buhari suna adawa da Tinubu basa so ya ci zabe, El-Rufai

A gefe guda, Gwamna Nasir El-Rufai ya yi zargin cewa akwai wasu na kusa da fadar shugaban kasa da basa son Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kai labari a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng