Mun San Abin da Muka Gani: Dalilin Hana Masoyan Tinubu Yin Gangami Inji ‘Yan Sanda
- ‘Yan sanda sun yi karin haske kan matsalar da aka samu wajen shirya gangamin Bola Tinubu
- Babban jami’in hulda da jama’a na dakarun ‘yan sanda ya fitar da jawabi a kan batun a makon nan
- Wasiu Abiodun ya ce bayanan sirri sun nuna masu hadarin taron da aka shirya, dole aka fasa shi
Abuja - Babban jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Najeriya, Wasiu Abiodun ya yi bayanin abin da ya faru da taron yakin zaben Bola Tinubu.
Leadership ta ce an shirya za ayi gangami domin nuna goyon baya ga 'dan takaran APC, Bola Tinubu a jihar Neja, amma dole aka dakata saboda wasu dalilai.
Wasiu Abiodun ya ce ‘yan sanda sun samu labari cewa akwai yiwuwar a kawo cikas ta fuskar tsaro, wannan ya sa suka dauki matakin dakile abin tun wuri.
“Dole ‘yan sanda suka karbe iko da wurin da aka shirya yin gangamin a matsayin matakin kariya saboda bayanan sirrin da muka samu na shirin tashin-tashina.
A dalilin haka, sai muka yi abin da ya dace wajen kauda yiwuwar kawo hari ko wasu tsageru suyi amfani da damar domin a tada hayaniya ko kawo fitina a cikin al’umma.”
- Wasiu Abiodun
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Akwai hannun Gwamna?
Rahoton The Nation ya ce Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ake zargin yana da hannu wajen hana taron, amma babu abin da ke tabbatar da zargin.
Sakataren yada labaran APC na jihar Neja, Alhaji Musa Sarkinkaji ya fitar da jawabi a ranar Litinin, yana cewa su ba su san da zaman taron da za ayi ba.
A jawabin na sa, Musa Sarkinkaji ya fadawa duk wasu ‘yan jam’iyya su kauracewa taron da aka yi nufin yi a garin New Bussa a karamar hukumar Borgu.
Legit.ng ta fahimci Shugaban APC na reshen jihar, Haliru Zakari Jikantoro ya fito daga shiyya daya da Sanata Sabi wanda ake rikici da shi a jam’iyyar.
Rikicin Gwamna da Sanatansa
Akwai sabani tsakanin Gwamna Abubakar Sani Bello mai takarar Sanatan Neja ta Arewa a zaben 2023 da Aliyu Sabi Abdullahi wanda ya yi niyyar taron.
Tun 2015, Sanata Aliyu Sabi shi ne Sanatan yankin da Mai girma Gwamnan ya fito (wanda wa’adin zai kare a Mayu), bai samu tikitin APC wannan karo ba.
Kamfen Tinubu a Kalaba
Labari ya zo cewa ‘Dan takaran Shugabancin Najeriya a Jam’iyyar APC a zaben bana, Bola Tinubu ya soki gwamnatinsu da kan shi a wajen yakin neman zabe.
An ji Tinubu yana cewa da sun gyara (darajar Naira) da yanzu mun yi nisa, basu san hanyar da za su bi ba, bisa dukkan alamu yana nufin Gwamnatin Buhari.
Asali: Legit.ng