Dan Takarar Gwamnan Jam’iyyar LP Ya Kauracewa Kamfen Din Peter Obi a Yola
- Gagarumin rikici ya kunno kai a jam’iyyar Labour Party reshen jihar Adamawa yan kwanaki kafin babban zaben 2023
- Dan takarar gwamnan LP a Adamawa da sauran masu neman mukaman siyasa sun kauracewa gangamin kamfen din Peter Obi
- Sun zargi kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar da mayar da su saniyar ware
Adamawa - Dan takarar gwamnan jam'iyyar Labour Party a jihar Adamawa, Umar Mustapha, da magoya bayansa sun kauracewa gangamin kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Peter Obi, a ranar Talata, 31 ga watan Janairu.
Obi, abokin takararsa, Datti Ahmed, Farfesa Pat Utomi da wasu hadimansa sun samu tarba daga tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawan a filin jirgin sama na Yola.
Baya ga Lawan da shugaban jam'iyyar na jihar, Christopher Nicholas, babu sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da suka je filin jirgin saman don tarbar dan takarar shugaban kasar na LP, jaridar Punch ta rahoto.
PDP ta janye ragamar abubuwa a jam'iyyar LP a Adamawa
A wata sanarwa da ke bayyana dalilinsu na kauracewa gangamin kamfen din Obi, Mustapha ya zargi shugabancin jam'iyyar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na LP da mayar da shi saniyar ware.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanarwar dauke da sa hannun Darakta Janar na kwamitin kamfen din Mustapha, Ibrahim Ghaji, ya kuma zargi jam’iyyar Peoples Democratic Party da janye ragamar harkokin LP a jihar, rahoton Vanguard.
Ghaji ya yi bayanin cewa bayan bitar ci gaban da ke jam'iyyar, dan takarar gwamnan da sauran yan takarar jam'iyyar sun yarda cewar ba za su shiga kowani harkoki na kamfen din da Obi zai yi a jihar ba.
Sai dai kuma, ya ce daukacin magoya bayan jam'iyyar da suka zabi halartan taron suna da zamar zuwa sannan su shiga a yi da su.
Sanarwar ta ce:
"Har ila yau, muna kuma yin Allah wadai da kwace harkokin jam'iyyar Labour Party da jam'iyyar Peoples Democratic Party, ta yi a jihar Adamawa.
"Wannan abun takaici ne kuma za mu yake shi, ta hanyar amfani da hanyoyin da suka dace, har sai mun ci nasara."
Daraktan yakin neman zaben Peter Obi ya sauya sheka zuwa PDP a jihar Bauchi
A wani labarin kuma, mun ji cewa Alhaji Alhassan Bawu, daraktan yakin neman zaben Peter Obi a jihar Bauchi da sauran jami'an jam'iyyar sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP ta su Atiku Abubakar.
Bawu ya bayyana cewa sun fice daga LP ne saboda basa son su yi asarar kuri'unsu kan mutumin da suka san ba zai taba lashe zabe ba.
Asali: Legit.ng