Bola Tinubu Ya Kuma Sukar Mulkin Shugaba Buhari a Gaban Jama’a Wajen Yawon Kamfe
- Da alama Asiwaju Bola Tinubu ya sake yin wasu kalaman da za su iya zama baram-barama
- ‘Dan takaran shugabancin kasar a zaben 2023 ya zargi gwamnati ta lalata tattalin arzikin kasa
- Bola Tinubu ya caccaki gwamnatinsu ta APC kan yadda $1 ta tashi daga N200 zuwa kusan N800
Cross River - Da jam’iyyar APC ta je yawon kamfe a jihar Kuros Ribas, Asiwaju Bola Tinubu ya nuna tattalin arzikin Najeriya yana a cikin matsala.
This Day ta fitar da rahoto a safiyar Laraba cewa Asiwaju Bola Tinubu ya zargi Gwamnatin Muhammadu Buhari game da rashin darajar Naira.
Abin ban mamakin shi ne ba a dade da ‘dan takaran kujerar shugaban kasar ya yi ta kokorin wanke kan shi daga zargin sukar gwamnati mai-ci ba.
Wannan karo, Bola Tinubu ya koka game da yadda darajar Dala take cigaba da lulawa sama, yayin da Naira ta ke karyewa a karkashin jagorancin APC.
Kudin Najeriya ya sukurkuce
A jawabin da ya yi a Kalaba watau babban birnin jihar Kuros Ribas, ‘dan takaran ya yi bayanin yadda Naira ta rasa N600 a kan Dalar Amurka a yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“A yau sun motsa da farashin canjin kudin (Dala) daga N200 zuwa N800. Da a ce sun gyara, sun shawo kan lamarin, da ba mu samu kanmu a halin nan ba.
Da sun gyara da yanzu mun yi nisa. Ba su san hanyar da za su bi ba, ba su san yadda za suyi tunani ba, ba su san yadda za su shawo kan lamarin ba.”
- Bola Tinubu
Bola Tinubu bai kama suna ba
A jawabinsa na jiya a garin Kalaba, babu inda tsohon Gwamnan na jihar Legas ya ambaci gwamnatin Muhammadu Buhari mai-ci ko jam’iyyarsu.
Ko da Tinubu bai kama suna ba, gwamnatin APC ce ta gaji Dala $1 a N200 daga hannun shugaba Goodluck Jonathan, yau Dala ta kai N700 a BDC.
Wadanda suka yi wa ‘dan takaran rakiya sun hada da Kashim Shettima wanda shi ne abokin gaminsa. A wajen an ji ya fadawa jama'a su gujewa PDP.
Tinubu ya tunawa wadanda suka halarci taron yadda ya maida Legas a lokacinsa, ya ce gwamnatinsa za ta kawo ayyukan yi, ta farfado da tattalin kasa.
Olusegun Awolowo ya samu aiki a AfCFTA
Femi Adesina ya bada sanarwa cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zabi Olusegun Awolowo, ya ba shi sakataren kujerar kwamitin AfCFTA.
Awolowo ya yi shekaru yana rike da Nigerian Export Promotion Council tun lokacin Jonathan. Sakataren kwamitin ya yi aiki a FCTA a Gwamnatin PDP.
Asali: Legit.ng