Surukin Buhari da Ya Sauya-Sheka Ya Fara Kamfe, Yana Kira a Guji APC a 2023
- Muhammad Sani Sha’aban ya fara yakin neman zama Gwamnan Kaduna a karkashin jam’iyyar ADP
- Hon. Sani Sha’aban ya kaddamar da kamfe a garin Tashar Yari, ya bukaci ‘Yan Kaduna su zabe shi a 2023
- ‘Dan siyasar ya yi alkawarin samar da tsaro, ya ce ba zai ci amanar jama’a idan ya shiga gidan gwamnati ba
Kaduna - Muhammad Sani Sha’aban wanda suruki ne a wajen Muhammadu Buhari ya soma yakin neman zama Gwamnan jihar Kaduna a zabe.
Hon. Muhammad Sani Sha’aban yana takarar Gwamnan Kaduna a karkashin jam’iyyar adawa ta ADP, biyo bayan sauya-shekarsa daga APC.
‘Dan siyasar wanda yana cikin wadanda suka kafa APC, ya bar jam’iyyar ne bayan rasa tikitin yin takarar Gwamna a 2023 a wajen Sanata Uba Sani.
Rahoton ya ce Sani Sha’aban ya kaddamar da yakin takararsa a garin Tashan Yari da ke karamar hukumar Makarfi, ya yi alkawarin yaki da talauci.
Alkawarin 'dan takarar jam’iyyar ADP
Idan jam’iyyar ADP ta kafa gwamnati a jihar Kaduna a Mayun 2023, ‘dan takaran ya sha alwashin yakar talauci da rashin tsaron da ya addabi al’umma.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hon. Sha’aban ya ce gwamnatinsa za ta ba manoma damar komawa gonakinsu.
Tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayyar na mazabar Zariya yake cewa ya shiga takarar Gwamnan ne domin ya taimakawa mutanen jihar Kaduna.
A cewar Sha’aban wanda ba yau ya fara takara ba, ya ce idan ya yi nasara a zabe mai zuwa, ba zai watsar da mutane kamar yadda ‘yan siyasa su ka saba ba.
Mafita ita ce ADP - Shugaban Jam'iyya
Kafin nan, an rahoto cewa shugaban jam’iyyar ADP na reshen Kaduna, Umar Isah ya ce mutanen jihar suna bukatar canji, kuma Sha’aban ne mafita a 2023.
Umar Isah ya yi kira da babbar murya da al’umma su yi waje da jam’iyyun APC da kuma PDP.
“Mutanen jihar Kaduna su na burin canji, kuma Sha’aban ne zai kawo sauyi da ake bukata a jihar. Mafita ita ce a kawo ADP da Sha’aban kurum a zabe mai zuwa.”
A dalilin haka mu ka tuntubi Siraj Bamalli, daya daga cikin matasan da ke goyon bayan takarar Isa Ashiru Kudan a jam'iyyar PDP a jihar Kaduna.
Malam Siraj Bamalli ya shaida cewa tsayawa takarar Sha'aban ba wata barazana ba ce a halin yanzu domin jam'iyyar da ya fito ba ta shahara sosai ba.
A game da sauran jam'iyyun hamayya da suka fito neman mulki a 2023, matashin ya ce tasirin LP zai bayyana ne kurum a fgaruwan Kudancin Kaduna.
Ban tsoron kowa - Wazirin Adamawa
A ranar Talata aka samu labari cewa Atiku Abubakar ya nuna akwai yiwuwar jam’iyyarsa ta hada-kai da Rabiu Kwankwaso ko Peter Obi a zaben bana.
A tattaunawar da aka yi da shi, babban ‘dan takaran kujerar shugabancin Najeriyan ya ce mutane sun gaji da mulkin APC, kuma ya tabo batun zargin rashawa.
Asali: Legit.ng