Babban Jigon Jam’iyyar LP a Jihar Bauchi Da Jami'an Jam'iyyar Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

Babban Jigon Jam’iyyar LP a Jihar Bauchi Da Jami'an Jam'iyyar Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

  • Jam'iyyar Labour Party ta rasa daya daga cikin manyan kusoshinta a jihar Bauchi gabannin babban zaben 2023
  • Daraktan yakin neman zaben Peter Obi a jihar, Alhaji Alhassan Bawu, ya fice zuwa jam’iyyar PDP
  • Bawo wanda ya fice tare da dumbin jami’an jam’iyyar a jihar ta arewa maso gabas ya ce jami’iyyar bata da wani tsari a jihar

Daraktan kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi a jihar Bauchi, Alhaji Alhassan Bawu, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP).

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Bawu wanda ya koma PDP tare da sauran jami'an jam'iyyar a jihar ta arewa maso gabas, ya daura laifin kan rashin tsarin jam'iyyar LP a matakan jiha, karamar hukuma da gudunma.

Peter Obi da Atiku Abubakar
Babban Jigon Jam’iyyar LP a Jihar Bauchi Da Jami'an Jam'iyyar Sun Sauya Sheka Zuwa PDP Hoto: Mr. Peter Obi/ Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Bawu ya ce:

Kara karanta wannan

Laifin APC Da Ganduje Ne Harin Da Aka Kaiwa Buhari a Kano, PDP Ta Tona Asiri

"Jam'iyyar LP bata da karfi kuma ba za ta iya kawo ko kujera guda daya ba a yankin."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mu na son bayar da kuri'unmu ne ga wanda zai iya cin zabe, Bawu

Da yake sanar da sauya shekarsa ga manema labarai a garin Bauchi, babban birnin jihar a ranar Talata, 31 ga watan Janairu, Bawa ya ce basa so su yi asarar kuri'unsu a zabe mai zuwa, rahoton Arise TV.

Ya ce:

"Ba ma so mu yi asarar kuri'unmu kuma muna son amfani da wannan lokacin wajen tattara kuri'u ga wanda zai iya cin zabe."

Ya ce dukkanin ciyamomin jam'iyyar, jami'an jihar da yankin da ma jami'an kasa daga yankin sun sauya sheka don marawa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar baya.

Akwai yuwuwar Kwankwaso ya janyewa Atiku a zaben 2023, kungiyar dattawan arewa

Kara karanta wannan

'Barin Zance: Gwamnonin APC 3 Sun Jagoranci Tinubu Domin Kai Wa Buhari Ziyarar Dannar Ƙirji

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu manyan masu ruwa da tsaki daga yankin arewacin kasar na kan tattaunawa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso domin su lallashe shi ya hakura da takararsa.

Kamar yadda rahotanni suka kawo, wani jigon arewa da aka sakaya sunansa ya ce akwai yuwuware Kwankwaso ya koma bayan takwaransa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a zaben na wata mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng