Ku Daina Shigar Mata: Aisha Binani Tayi Kira ga Masoyanta Da Ke Mata 'Kara'

Ku Daina Shigar Mata: Aisha Binani Tayi Kira ga Masoyanta Da Ke Mata 'Kara'

  • Aishatu Ahmed Binani, 'yar takarar gwamna a jam'iyyar APC a jihar Adamawa ta yi kira ga magoya bayanta da su taimaka su dinga shiga irin ta jinsinsu
  • A cewarta, ta na matukar ganin girman maza don haka su taimaka su tsaya a matsayinsu na maza wanda suke tuntuni
  • 'Yar takarar mai dumbin magoya baya ta yi kira ga masoyanta da su zabeta da duk wani 'dan takarar APC daga sama har kasa

Adamawa - 'Yar takarar gwamnan jihar Adamawa karkashin jam'iyyar APC, Sanata Aishatu Ahmed Binani ta roki magoya bayanta da su taimaka su dinga shiga irin ta jinsinsu kamar yadda Ubangiji ya yi umarni.

Aisha Binani
Ku Dain Shigar Mata: Aisha Binani Tayi Kira ga Masoyanta Da Ke Mata 'Kara'. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Kai tsaye ta roki mazan da ke shigar mata a zagayen kamfen din ta ko wani taro da ya yi kama da haka da su daina wannan dabi'ar.

Kara karanta wannan

Bidiyo:Matar aure ta Kama Mijinta Dumu-dumu da Budurwarsa a Wurin Cin Abinci, An Tafka Dirama

Jaridar The Nation ta ruwaito yadda matasa maza da dama saboda tsabar goyon bayan Binani da suke suka koma shigar mata don taya murnar yadda Binani ta kasance mace tilo da ke takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC.

Sai dai, bata yaba da wannan dabi'ar ba a zagayen kamfen din ta a karamar hukumar Gombi na jihar a karshen wannan makon.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin godiya ga mutane bisa goyon bayan da suka bata, ta roki wadanda suke shigar mata da su daina, tana ganin girman duk maza saboda haka tana sa ran maza su tsaya a maza.

Ta roki mutanen Gombi da su fito su kada ma ta kuri'u da sauran 'yan takarar APC daga sama har kasa.

'Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Gombi da Hong, Yusuf Captain Buba, ya roki mutanen Gombi da su kada kuri'unsu ga Binani da duk wani 'dan takarar APC don cigaba da morar romon dimokaradiyya.

Kara karanta wannan

Amarya Ta Antayawa Uwarginta Tafasashen Ruwa Kan Zargin Maita A Jihar Kwara

Haka zalika, yayin jawabi, fitacciyar mai marawa Binani baya, Ambasada Fati Balla ta ce yanzu lokaci ya yi da za a ba mace damar jagorantar jihar Adamawa, inda za ta zamo mace ta farko da aka zaba a matsayin gwamna.

A cewarta, Binani ta cancanci kujerar bayan irin namijin kokarin da tayi a mukaman gwamnati da dama, na farko a matsayin 'yar majalisar da kuma a matsayin sanata.

Buhari da Tinubu sun daga hannun Binani a Adamawa, sun ce zabe ta

A wani labari na daban, hotunan shugaba Buhari da Tinubu a jihar Adamawa sun bayyana inda suka je gangamin kaddamar da kamfen din Bola Tinubu da Aisha Binani.

Gogaggun 'yan siyasan sun daga hannu Aisha Binani sama inda suka bukaci jama'a da su zabe kallabin tsakanin rawuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel