Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Mai Magana da Yawun Majalisar Tarayya

Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Mai Magana da Yawun Majalisar Tarayya

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun kai hari ofishin mai magana da yawun majalisar wakilai, Benjamin Kalu, a Uzuakoli, yankin Bende da ke jihar Abia
  • Kalu ya bayyana cewa an ga harsashi fiye da 100 bayan maharan sun bar wajen inda suka lalata ginin
  • Dan majalisar ya ce babu jami'in tsaro ko guda a wajen har sai bayan da yan bindigar suka wuce, yana mai cewa an kai rahoton lamarin ga yan sanda a Uzuakoli

Abia - Wasu yan bindiga da ba a san ko wanene ba sun kai hari ofishin Benjamin Kalu, mai magana da yawun majalisar wakilai na mazabarsa da ke yankin Bende a jihar Abia.

Yayin da yake Allah wadai da harin a wata hira da manema labarai a ranar Asabar, 28 ga watan Janairu, Kalu ya bayyana lamarin a matsayin aikin matsorata, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Fitaccen Malamin Addini Na Najeriya Ya Bayyana Yan Takarar Shugaban Kasa Da Za Su Fadi Zabe

Benjamin Kalu da yan bindiga
Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Kakakin Majalisar Tarayya Hoto: Benjamin Kalu
Asali: Twitter

Dalilin da yasa yan bindiga suka farmaki ofishin mai magana da yawun majalisa

A cewar dan majalisar, an gano harsasai fiye da 100 bayan maharan sun bar wajen, yana mai cewa sun lalata ginin, rahoton Daily Trust.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, dan majalisar bai ce an rasa rai ba amma ya bayyana cewa babu kowani jami'in tsaro har sai da yan bindigar suka bar wajen. Ya kara da cewar an kai rahoton lamarin ofishin yan sanda a Uzuakoli.

Dan majalisar ya ce:

"An farmaki ofishin da misalin 10:00 da ya mintuna na dare. Fiye da harsasai 100 aka gani, inda suka lalata winduna da saman silin. An ciccire alunan All Progressives Congress (APC) sannan aka farfasa su.
"Babu jami'in tsaro ko daya har sai bayan da suka wuce. Hadimai na sun kai rahoton lamarin ofishin yan sandan Uzuakoli reshen Bende. Ina mai son cewa don ci gaban damokradiyyarmu, rikici ba abun yi bane."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Babban Bakin Ciki, Hawaye Yayin Da Yan Bindiga Suka Kashe Fitaccen Malamin Addini A Jihar Arewacin Najeriya

Ya kuma yi kira ga magoya bayansu a kan su ci gaba da sanya rai ga nasara saboda sun fara da kyau kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba.

Ni ne zan lashe zabe duk da bita da kullin da ake yi mun, Tinubu

A wani labarin, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya ce su ne za su lashe zaben wata mai zuwa duk da zagon kasa da ake yi masu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel