Gwamnonin G5 Sun Bayyana Yan Takarar da Zasu Marawa Baya a Enugu, Sun Yi Gum Kan Atiku
- Gwamnonin tawagar G-5 sun ayyana goyon bayansu ga dukkan 'yan takarar jam'iyyar PDP na jihar Enugu
- Tawagar, karkashin jagorancin gwamna Wike na jihar Ribas ta yi gum game da Atiku a Ralin da ya gudana ranar Jumu'a
- Har yanzu dai ba'a ga maciji tsakanin ɓangaren Atiku Abubakar da gwamna Wike tun bayan zaben fidda gwani
Enugu - Mambobin tawagar gwamnonin G-5 sun ayyana cikakken goyon bayansu ga 'yan takarar jam'iyyar PDP a jihar Enugu.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa gwamnonin sun bayyana haka ne a wurin Ralin yakin neman zaɓen PDP wanda ya gudana a Enugu jiya Jumu'a.
Tawagar G-5, ta ƙunshi wasu gwamnonin jam'iyyar APC da suka fusata karƙashin jagorancin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Bayan Wike, sauran gwamnonin da suka haɗa tawagar sun ƙunshi, Samuel Ortom (Benuwai), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Seyi Makinde (Oyo) da takwaransu na jihar Abiya, Okezie Ikpeazu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin sun bukaci shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus a ɗora ɗan kudu sabida a yi wa kowane yanki adalci. Sun ce Atiku da Ayu duk yan arewa ne.
Goyom bayan yan takarar PDP na jihar Enugu
Jam'iyyar PDP ta bayyana tare da miƙa tuta ga dukkanin 'yan takararta na jihar Enugu a ralin da aka shirya a fitaccen filin wasan nan, Michael Okpara Square, Enugu.
Banda Sanata Chimaroke Nnamani, ɗan takarar PDP a mazaɓar Enugu ta gabas, dukkan 'yan takarar jam'iyyar a jihar kama daga ɗan takarar gwamna, majalisar wakilai, Sanatoci da majalisar jiha duk sun karɓi tuta a Ralin.
Sanata Nnamani da aka nema aka rasa a wurin taron, PDP ta dakatar da shi a baya-bayan nan bisa zargin yi wa jam'iyya zagon ƙasa, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Gwamnonin G-5 a wurin taron sun bayyana goyon bayansu ga baki ɗaya 'yan takaran amma sun yi gum da bakinsu game da Atiku Abubakar, mai neman zama shugaban kasa a inuwar PDP.
Gwamnan Abiya ne kaɗai bai je Ralin ba daga cikin mambobin G5 kuma hakan na da alaƙa ne da mutuwar ɗan takarar gwamnan PDP, Uchenna Ikonne, wanda ya zaɓi ya gaje shi.
"Ina tabbatar maku zamu wa ɗan takarar gwamna Addu'a, mataimakinsa, abokinmu Ugwuanyi wanda ke neman Sanata, da sauran 'yan takarar majalisar wakilai da ta jiha."
"Zamu ba ku duk gudummuwar da ake bukata kuma zamu tabbatar kun samu nasara a zabukan dake tafe ranar 25 ga watan Fabrairu da 11 ga watan Maris, 2023."
- Inji Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas a madadin G-5.
A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Shugabanta Na Jihar Ebonyi Kan Cin Amana
Mai magana da yawun PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a 27 ga watan Janairu, 2023.
Yace a halin yanzu shugaban PDP na Ebonyi da aka dakatar zai gurfana a gaban kwamitin ladabtarea domin ɗaukar mataki na gaba a kansa.
Asali: Legit.ng