2023: An Bayyana Wasu Jihohi 12 da Ake Tunanin Za a Tafka Magudi a Zabe Mai Zuwa

2023: An Bayyana Wasu Jihohi 12 da Ake Tunanin Za a Tafka Magudi a Zabe Mai Zuwa

  • Wani bincike da aka gudanar ya nuna magudin zabe zai fi yawa a wasu jihohin Arewa da Neja-Delta
  • Yiaga Africa, The Kukah Centre; Enough is Enough Nigeria, su na cikin wadanda suke yi binciken
  • Ana tunanin ba za a samu yawaitar magudin zabe a jihohi irinsu Gombe, Ondo da birnin Abuja ba

Nigeria - Saura kasa da wata daya a shirya babban zabe a Najeriya, mutane a duk fadin jihohin kasar nan za su fita domin zaben sabon shugabansu.

Wasu kungiyoyi masu zaman kansu, sun gudanar da bincike wanda ya nuna masu akwai jihohi har 22 da akwai matukar yiwuwar a tafka magudin zabe.

Vanguard ta ce wadannan kungiyoyi goma su na tsoron za ayi satar kuri’u da sauran abubuwan da suka sabawa doka a jihohin nan zabukan da za a shirya.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Fitaccen Malamin Addini Na Najeriya Ya Bayyana Yan Takarar Shugaban Kasa Da Za Su Fadi Zabe

Akwai jihohi uku da binciken ya nuna cewa magudi da murdiyar da za a jarraba, za su yi kamari ba.

Su wanene suka yi binciken?

Kungiyoyin da suka gabatar da wannan bincike sun hada da International Press Centre; Institute for Media and Society; da Partners for Electoral Reform.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sannan akwai Nigerian Women Trust Fund; The Kukah Centre; Enough is Enough Nigeria; da cibiyar Center for Journalism Innovation and Development.

Zaben Najeriya
Ana zabe a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Rahoton ya ce akwai SBM Intelligence; Dataphyte; Yiaga Africa da gidauniyar Albino Foundation.

Daga cikin wadanda suka halarci taron nan akwai Samson Itodo, Dr. Akin Akingbulu, Samson Ezenwa, Misis Cynthia Mbamalu, da Emmanuela Azu.

A gaban Lanre Arogundade, Yemi Adamilekun da Jack Epelle aka gabatar da wannan rahoto.

Jihohin da za a yi magudi

Binciken na EMRI ya nuna mafi yawan jihohin da za a iya murde zabe su na Arewa ne: Borno, Yobe, Nasarawa, Benuwai, Kogi, Zamfara, da Kebbi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Babban Bakin Ciki, Hawaye Yayin Da Yan Bindiga Suka Kashe Fitaccen Malamin Addini A Jihar Arewacin Najeriya

Ragowar su ne Delta, Bayelsa, Edo da Kuros Riba duk a yankin Kudu maso kudancin Najeriya. Punch ta ce jihar karshe ita ce Ogun a Kudu maso yamma.

Idan binciken ya tabbata, Jihohin da magudi zai karanta su ne Gombe, Ondo sai babban birnin tarayya Abuja. Ana sa ran ayi zaben gaskiya a yankunan.

NNPP ta na kuka da INEC

A wani rahoto da muka fitar a yammacin Juma’a, an ji Kakakin New Nigeria People’s Party (NNPP) ya zargi INEC da kin bin hukuncin kotun daukaka kara.

Dr. Agbo Major ya shaidawa manema labarai, Hukumar INEC ta ki karban canjin wasu ‘yan takaransu na 2023 da suka yi murabus ko suka sauya-sheka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng