Motar Kudi da Aka Gani a Gidan Tinubu Batan Hanya Tayi, Jigon APC

Motar Kudi da Aka Gani a Gidan Tinubu Batan Hanya Tayi, Jigon APC

  • Sakataren shirye-shirye na APC, Ayodele Adewale, yace motocin kudi da suka shiga gidan Tinubu ana jajiberin zabe batan kai suka yi
  • Ya tabbatar da cewa yana cikin gidan kuma ba nan ya dace su shiga ba, adireshin ne suka yi makuwa suka fada cikin gidan Tinubu
  • Duk da Tinubu da kansa ya amsa cewa kudi ne shakare, Adewale yace ba'a ce kawai Tinubu yayi amma ba gaskiya bane lamarin

Legas - Ayodele Adewale, sakataren shirye-shirye na jam'iyyar APC a jihar Legas, yace motar kudin da aka gani ta shiga gidan Bola Tinubu a 2019 ta yi batan kai ne, ba nan tayi niyyar zuwa ba.

Sa'o'i kafin zaben 2019, an ga hotuna a soshiyal midiya inda motocin daukar kudi daga banki guda biyu suka shiga gidan Tinubu.

Kara karanta wannan

Ya fasa kwai: Tinubu ya fadi makarkashin yin sabbin Naira da karancin mai a Najeriya

Motocin kudi
Motar Kudi da Aka Gani a Gidan Tinubu Batan Hanya Tayi, Jigon APC. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

An dinga rade-radin kan abinda ke cikin abun hawa inda wasu da yaa ke cewa takardun dangwale ne na kada kuri'a yayin da wasu suka dinga ikirarin kudi ne shakare.

Jaridar TheCable ta rahoto cewa, Tinubu yace ababen hawan dankare suke da kudi ba takardun dangwala kuri'a ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin zantawa da Arise TV a ranar Alhamis, Adewale yace Tinubu wanda yanzu shi ne 'dan takarar shugaban kasa na APC, wasa ya ke da yace abinda ke cikin motocin kudi ne.

"Kan batun motocin bankin, ina tunanin an kammala zance. Babu kudi a cikin wadannan motocin kuma batan kai ma suka yi suka shiga gidansa."

- Yace.

"Motocin kudi basu yi aiki ba ranar zaben. Ina gidan a ranar nan. Wadannan motocin kudin batan kai suka yi suka shiga gida. Ba Asiwaju ko wani ne ya gayyacesu ba.

Kara karanta wannan

Uwa Ta Fasa Asusun Yaranta Bayan Shekaru 10, Ta Fitar Da Tsoffin Kudi a Bidiyo

"Abinda yace kan kudi a cikin motocin duk wasa yake yi. Ya fada ne cike da ba'a. Kamar yadda Dangote yace a yayin da yake son tantancewa yana da kudi da gaske, ya je ya cire miliyan daya, ya zauna ya kalla kuma ya mayar dasu bankin."

- Ya kara da cewa.

Fusatattun matasa sun balle zanga-zanga a Katsina

A wani labari na daban, fusatattun masata a Kofar Kaura a jihar Katsina sun barke da zang-zanga jim kadan bayan Buhari ya kaddamar da gadar sama.

Sun fara kone-kone tare da ihun ba mu yi da jifan jami'an tsaro da motocin APC bayan Buhari ya bar wurin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel