Kwamishina Ya Musanta Rahoton Masari Ya Cire Kusan Miliyan N500m Don Tarban Buhari
- Hon Yau Umar Gwajo-Gwajo ya musanta rahoton dake yawo cewa za'a kwashi kuɗin Gwamnati a tarbi shugaba Buhari
- Wata takarda ta nuna cewa Masari ya amince ta rage wa aljihun kananan hukumomin Katsina ƙiɓa don tara mutane
- Kwamishinan kanan hukumomi yace ko kaɗan labarin ba gaskiya bane domin bai iso Ofishinsa ba
Katsina - Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin Sarauta, Ya’u Umar Gwajo-gwajo, ya musanta rahoton dake yawo cewa Gwamna Aminu Masari ya ware wasu kudade domin tarban shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Gwajo-Gwajo ya karyata rahoton da ke cewa Masari ya amince da ware miliyan N499.6m domin ɗaukar nauyun mutane su fito yi wa shugaban ƙasa maraba yayin ziyarar da zai kawo Katsina.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai kai ziyara jiharsa ta Katsina domin kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatin Masari ta kammala.
Da yake martani kan zargin ware kuɗin kusan miliyan N500m, Kwamishinan ya yi fatali da labarin amincewar Masari ko zare kuɗin daga asusun gwamnatin jihar Katsina.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewarsa, a 'yan kwanakin nan ya maida hankali kan harkokin yakin neman zabe sakamkon haka ba ya samun lokacin zama a Ofishinsa.
A kalamansa yayin da yan jarida suna nemi jin tabbacin lamarin, Honorabul Gwajo-Gwajo ya ce:
"A iya sani na, babu wasu kuɗi da aka amince da ware su ko aka zare su daga Aljihun gwamnati. Baya ga haka ina wurin harkokin kamfen ɗan takararmu, ban samu zuwa Ofis ba balle na duba Fayil-Fayil a kwanakin nan."
"Wasu daga cikinku (yan jarida) da suke bibiyarmu wurin kamfe zasu ba da shaida kan haka. Abu na biyu babu wanda ya ankarar da ni cewa akwai wata takarda da ke bukatar na duba ta."
Raɗe-raɗin Masari ya ware makudan kuɗin domin ziyarar Buhari ya fasu ne a wata wasika da ta bayyana mai ɗauke da kwanan watan 18 ga watan Janairu, 2023, kamar yadda Ripples ta ruwaito.
Wasikar na ɗauke da sa hannunYahuza S. Ibrahim a madadin babban Sakataren gidan gwamnatin Katsina kuma an aikata ne zuwa ga kwamishinan kananan hukumomi.
A cewar takardar wacce ta yi yawo a kafafen sada zumunta, za'a ɗauki kuɗaɗen ne daga cikin kasafin kananan hukumomi na jihar Katsina.
Rigingimun APC sun ƙara tsananta
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Kori Tsohon Hadimin Shugaban Kasa Buhari Kan Zargin Ɗaya da Take Masa
Wata wasika da ta fasu a Intanet ta nuna cewa APC reshen jihar Akwa Ibom ta ƙori Sanata Ita Enang daga inuwarta kwanaki kaɗan bayan Kotu ta yanke hukunci.
Wasiƙar na ɗauke da sa hannun shugaban APC na jihar Akwa Ibom, Stephen Ntukekpo, da kwanan watan 24 ga watan Janairu, 2023.
Asali: Legit.ng