An Kai wa Tawagar ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Hari Sau 2 Wajen Yawon Kamfe
- Peter Obi ya bada labarin yadda aka auka masa da duwatsu da ya je yawon yakin zabe a garin Katsina
- Wani jawabi ta bakin sashen yada labaran kwamitin kamfe ya ce an kai harin ne a yammacin Litinin
- Diran Onifade ya ce ‘yan adawan Arewa maso yamma ne suka razana da yadda Obi yake karbuwa
Katsina - Peter Obi mai neman zama shugaban kasa ya bada labarin yadda aka kai wa tawagarsa hari a lokacin da suka ziyarci jihar Katsina.
A yammacin Talata, Daily Trust ta rahoto ‘dan takaran kujerar shugabancin Najeriya a jam’iyyar LP yana cewa an kai masa hari a wajen kamfe.
A wani jawabi da ya fitar ta bakin Diran Onifade, ‘dan takaran ya yi Allah-wadai da abin ya faru da shi da mutanensa da suka je taron siyasa jiya.
Shugaban sashen yada labaran kwamitin yakin neman zaben Obi/Datti ‘yan iskan gari sun auka masu da duwatsu ne a kan hanyar zuwa filin jirgi.
Jawabin Diran Onifade
“’Dan takaranmu ya hadu da mata a wajen taro, daga nan sai ya halarci gangami a filin wasa na Muhammad Dikko, aka tashi lafiya kalau.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Amma a kan hanyarsa ta zuwa filin tashi da saukar jirgin sama, sai wasu ‘yan iskan-gari suka kai wa motar ‘dan takaranmu hari da duwatsu.
Sun aukawa bangaren kujerar direba, a dalilin haka suka yi wa motar illa sosai.
- Diran Onifade
Abin da rahoton Blueprint ya nuna, an taki sa'a domin kuwa ‘dan takaran na 2023 da duk abokan tafiyarsa ba su samu wani rauni a dalilin hakan ba.
Duwatsu a wajen filin wasa
Da Duminsa: Sabuwar Kungiyar ‘Yan Ta’adda Ta Bullo a Kudu, Sun Gindaya Sharadi Kafin Su Bari ayi Zabe
Onifade ya kara da cewa an samu wasu ‘yan iskan da suka rutsa su da duwatsu a wajen filin wasan, hakan ya jawo lalata motocin kamfe da-dama.
A cewar kwamitin yakin zaben, wasu ‘yan siyasa da suke tunanin LP ba ta da karfi a Arewa maso yamma ne suka tsorata da irin farin jinin Obi a yankin.
A karshen jawabin, kwamitin ya yabawa Katsinawan da suka nunawa ‘dan takaran na LP kauna, sannan aka bukaci jami’an tsaro su binciki lamarin.
Rikicin cikin gida a LP
Ku na da labarin yadda Jam’iyyar adawa ta LP ta shiga rudani a gabar yakin neman zaben shugaban kasa a jihar Kano saboda sabanin da aka samu.
Bashir I. Bashir, Mohammed Zarewa, Balarabe Wakili da Idris Dambazau sun kauracewa Peter Obi da ya je kamfe saboda rikicin da ake yi a LP.
Asali: Legit.ng