Dan Takarar Jam'iyyar PDP Da Ake Nema Ruwa A Jallo Ya Fito Ya Yi Magana

Dan Takarar Jam'iyyar PDP Da Ake Nema Ruwa A Jallo Ya Fito Ya Yi Magana

  • Ɗan takarar majalisar wakilan tarayya na PDP a jihar Kuros Riba yace Abinda hukumar yan sanda ta yi siyasa ce
  • Hukumar yan sandan jihar ta ayyana neman Peter Akpanke ruwa a jallo bisa zargin hannu a kisan Insufektan yan sanda
  • A cewar ɗan takarar an kirkiri nemansa ne domin ɗauke masa hankali yayin da babban zabe ke kara matsowa

Cross River - Peter Akpanke, ɗan takarar majalisar tarayya na jam'iyyar PDP a jihar Kuros Riba, yace ayyana nemansa ruwa a jallo da hukumar 'yan sanda ta yi siyasa ce.

Ɗan siyasan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ta hannun lauyansa, Mba Ukweni, kuma aka raba wa manema labarai a Kalaba ranar Litinin.

Jam'iyyar APC.
Dan Takarar Jam'iyyar PDP Da Ake Nema Ruwa A Jallo Ya Fito Ya Yi Magana Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

Jaridar Premium Times ta rahoto Mista Akpanke na cewa duk da hukumar ta yi haka ne domin ɗauke masa hankali daga shirin zaɓen 2023, yana nan daram bai damu da tsoratarwan ba.

Kara karanta wannan

2023: Wata Ɗaya Kafin Zabe, Atiku da PDP Sun Samu Gagarumar Nasara a Jihar Tinubu

A wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na hukumar yan sandan Kuros Riba, Irene Ugbo, ya fitar ta ayyana neman ɗan takarar ruwa a jallo bisa zargin hannu a kisan Insufekta Emmanuel Martin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An harbe Mista Martin har lahira a ranar 25 ga watan Mayu, 2022 a garin Obudu, dake kudancin Kuros Riba lokacin zaɓen fidda gwanin PDP na takarar majalisar wakilai.

Amma lauyan ɗan takarar, Mista Ukweni, ya ce Kes din wanda yake wa aiki, mai neman zama mamba mai wakiltar mazaɓar Obudu, Bekwarra & Obanliku, "Siyasa ce da aka kirkira da nufin ɗauke masa hankali daga zaɓe."

"Akpanke ba ya tsoron shari'a amma maganar gaskiya ita ce bai aikata komai ba, mutumin da ya aikata ɗanyen aikin nan an kama shi kuma an miƙa wa yan sanda."
"Abun takaicin wanda ya tura waɗanda suka sheke ɗan sandan an kyale shi, wanda ya yi kisan kuma yana samun kariya daga gwamna, kuma Antoni Janar ya killace shari'ar."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Kama Shugaban APC da Wasu Mutane Sama da 20 Da Hannu a Kashe-Kashen Rayuka

"Zamu iya bayyana wa duniya abinda muka gano a binciken mu, majiya mai karfi ta bamu bidiyon da aka ɗauki mutumin da ake zargi da kisan Insufekta yayin da jami'ai ke tuhumarsa da bayanan da ya bayar."

Daga karshe, ɗan siyasan ya ce babu gayyatar da 'yan sanda suka aiko masa ya yi kunnen uwat shegu, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Yan daba sun kai wa ayarin ɗan takarar gwamna hari

A wani labarin kuma Miyagu Sun Farmaki Dan Takarar Gwamna a Jihar Ribas, Sun Tafka Barna

Rahotanni daga jihar Ribas sun tabbatar da cewa wasu yan baranda sun bude wa ayarin ɗan takarar gwamna wuta a jihar Rabas ranar Asabar da ta gabata.

Ɗan takaran wanda ya tsira daga harin, ya nuna danuwarsa kan yadda siyasar Ribas ke sauya akala zuwa ta zubda jini.

Asali: Legit.ng

Online view pixel