Kotu ta Saka Ranar Yanke Hukuncin Karshe kan Zaben Gwamnan Osun

Kotu ta Saka Ranar Yanke Hukuncin Karshe kan Zaben Gwamnan Osun

  • Kotun sauraron kararrakin zabe da ka zama a jihar Osun ta sanar da cewa za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar da aka yi na 2022
  • Kamar yadda takardar da kotun ta lika a gaban dakin kotun, tace za ta fara zaman kotun da karfe 9 na safiyar 27 ga watan Janairun 2022
  • Tsohon gwamnan jihar, Oyetola tare da jam'iyyar APC ta maka Adeleke a kotu kan zargin aringizon kuri'u a zaben jihar da ya gabata wanda yayi nasara

Osun - Kotun sauraron kararrakin zabe na gwamnan jihar Osun ta saka ranar 27 ga watan Janairun 2023 domin yanke hukunci.

Zaben Osun
Kotu ta Saka Ranar Yanke Hukuncin Karshe kan Zaben Gwamnan Osun
Asali: Original

Kamar yadda takardar da aka manna a hanyar shiga kotun ta nuna, tace za a fara zaman kotun da karfe 9 na safe a ranar, jaridar TheCable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jam'iyyar APC Ta Yi Martani Kan Yunkurin Da PDP Ta Yi Na Haramtawa Tinubu Takara

A watan Augustan 2022, Gboyega Oyetola, tsohon gwamnan jihar Osun da jam'iyyar APC ta kai korafi gaban kotun inda ta kalubalanci nasarar Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP.

Daga cikin matsalolin, Oyetola ya zargi cewa akwai batun aringizon kuri'u a rumfunan zabe 749 da ke kananan hukumomi 10 na jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A yayin jawabi kan abinda ya ke tsammani, Adeleke, Gwamnan jihar Osun yace yana da tabbacin samun nasara a kotun.

A bangaren jam'iyyar APC reshen jihar Osun, tayi umarni ga mambobinta da su fara azumin kwanaki bakwai da addu'a domin samun nasara a kotun.

A daya bangaren, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, tace Adeleke zai ci zaben ko da kuwa ba a hada sakamakon da na rumfunan zaben Oyetola ba.

Hukumar zabe a jawabin karshe da Paul Ananaba ya rubuta, lauyan hukumar, ya jaddada cewa Adeleke ne ya ci zaben gwamnonin.

Kara karanta wannan

Kotun Daukaka Kara Ta Kori Ɗan Takarar Gwamnan APC a Jihar Arewa, Ta Umarci a Sake Zabe a Yankuna 11

"Masu korafin sun yi korafi kan aringizon kuri'u daga rumfunan zabe 749 daga cikin 1,750, kamar yadda mai korafi na farko ya bayyana,"

-Anananba ya sanar.

Idan aka cire rumfunan zabe 1,750 daga 3,763 a jihar, wanda ake kara na biyu zai kasance wanda yayi nasara da sama da kuri'u 20,000.

Bayan barin APC, Sanata Naja'atu ta gana da Atiku

A wani labari na daban, Sanata Naja'atu Muhammad ta saka labule da Atiku Abubakar, 'dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP.

Naja'atu cikin makon da ya gabata ta fice daga jam'iyyar APC tare da yin watsi da mukamin daraktan kamfen da Tinubu ya bata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng