Mutum Miliyan 7 da ke Goyon Buhari da Osinbajo Za Su Koma PDP Nan da 'Yan Awanni
- An samu mutum miliyan bakwai masu katin zabe da suka dawo daga rakiyar jam’iyyar APC
- Raymond Dokpesi ya sanar da haka a wata wasika da ya aika zuwa ga Gwamna Ifeanyi Okowa
- Babban jagoran na jam’iyyar PDP yana so Okowa ya ba tsofaffin ‘ya ‘yan APC muhimmanci
Abuja - Shugaban kamfanin sadarwa na Daar Communications, Raymond Dokpesi ya ce akwai dinbin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC da ke neman komawa PDP.
The Cable ta ce Raymond Dokpesi ya rubuta wasika zuwa ga Gwamna Ifeanyi Okowa, ya sanar da shi halin da wasu magoya bayan jam’iyyar APC suke ciki.
Kamar yadda aka sani, Ifeanyi Okowa shi ne ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP.
A wasikar da aka rubuta a ranar Asabar, 21 ga watan Junairu 2023, Raymond Dokpesi ya ankarar da gwamnan na Delta cewa ‘ya ‘yan APC za su shigo PDP.
Gangamin Garin Asaba
A cewar Dokpesi, wadannan ‘yan APC da suke goyon Muhammadu Buhari da Yemi Osinbajo za su sanar da sauya-shekarsu wajen taron PDP da za a shirya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ranar Talata mai zuwa, Jam’iyyar adawa ta PDP ta ke shirin gudanar da babban taron siyasa a Delta – mahaifar ‘dan takaran mataimakin shugaban kasa.
Wasikar Dokpesi ta shaidawa Gwamna Okowa cewa bayan sun yi bincike da kyau, sun gano adadin masu shirin sauya-shekar sun haura miliyan bakwai.
An rahoto Dokpesi yana ba Okowa shawarar ya ba tsofaffin ‘ya ‘yan na APC matsayi na musamman.
Abin da wasikar Raymond Dokpesi ta kunsa
"Mai girma Gwamna, za ka samu wasika daga tsofaffin ‘yan kungiyoyin magoya bayan Muhammadu Buhari/Temi Osinbajo a fadin Najerya da suke sha’awar shawa sheka daga APC zuwa PDP a wajen gangamin kamfe da za ayi a garin Asaba a ranar Talata, 24 ga watan Junairu.
Mun yi bincikenmu a kan su, mun gano lallai adadinsu ya kai mutum miliyan bakwai masu rajistar zabe. Su na da karfi sosai a yankin Kudu maso kudu.
An sanar ni da cewa domin a rage dawainiyarsu, za su aiko da wakilai uku daga kowace jiha da mutum 20 daga cikin shugabanninsu zuwa garin Asaba."
- Raymond Dokpesi
PDP za ta lashe zaben 2023 - PCC
An ji labari Kwamitin takaran Atiku Abubakar ya kamata Obafemi Awolowo da Bola Tinubu, don haka ya ce PDP za ta ci zabe kamar yadda NPN tayi a 1979.
Dele Momodu yana ganin Peter Obi shi ne tamkar Nnamdi Azikiwe, sai ya kara da cewa Rabiu Kwankwaso ne tamkar Marigayi Malam Aminu Kano a yau.
Asali: Legit.ng