Na Yi Alkawarin Zan Yi Wa Yan Najeriya Aiki Iya Karfina, Shugaba Buhari
- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kai ziyara fadar mai martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Adamu
- Shugaban ya ce a lokacin kamfe ya yi alkwarin yi wa Najeriya da mutanen cikinta aiki daidai karfinsa
- Shugaban APC na ƙasa, Sanata Ahmad Lawan, Femi Gbajabiamila, Tinubu da Shettima na cikin tawagar Buhari
Bauchi - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce ya ɗauki alƙawari tun a baya cewa zai bauta wa Najeriya da mutanen da ke cikinta iyakar karfinsa.
Shugaba Buhari ya yi wannan furucin ne yayin da ya kai ziyarar gaisuwa ga Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Adamu, a wani ɓangare na Ralin ɗan takarar shugaban kasa na APC a Bauchi.
Vanguard ta rahoto Buhari na cewa:
"A 2003 da 2012 na kai ziyara baki ɗaya kananan hukumomi 774 da ke ƙasar nan. A 2019 lokacin da nake neman tazarce na samu ikon zuwa baki ɗaya jihohin Najeriya."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Saboda haka a nan ne na ɗauki alkawari kuma na sha alwashin zan yi wa Najeriya da yan ƙasa aiki bakin karfin da Allah ya bani."
Shugaban ƙasan wanda ya nuna jin daɗinsa da irin tarbar da aka masa a fadar Sarkin, ya gaba wa gwamna Bala Muhammed bisa ayyukan alherin da ya zuba wa al'umma a Bauchi.
Da yake jawabi, Sarkin Bauchi ya miƙa godiyarsa ga shugaban kasa bisa wannan ziyara da ya kai masa kana ya roki 'yan siyasa da su yi siyasa babu gaba.
Yayin da yake yaba wa Ƙauran Bauchi bisa baiwa kowace jam'iyyar siyasa dama a Bauchi, Basaraken ya yi wa shugaban kasa Addu'ar Allah ya sauke shi lafiya.
The Nation ta ruwaito cewa Buhari ya ziyarci fadar Sarkin ne tare da rakiyar shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, da kakakin majalisa, Femi Gbajabiamila.
Sauran sun haɗa da dan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, abokin takararsa, Kashim Shettima, da sauran jiga-jigan siyasa.
Matsala ta faru a taron APC na Bauchi
A wani labarin kuma An Shiga Rudani Yayin da Gangamin APC Ya Zo Karshe Ba Zato Ba Tsammani
Rahotanni sun bayyana ana tsaka da taron ne sauti ya ɗauke kuma duk kokarin shawo kan lamarin ya ci tura.
Hakan ya tilastawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya halarci gangamin barin wajen tare da mukarrabansa.
Asali: Legit.ng