An Kawo Karshen Gangamin Yakin Neman Zaben APC a Bauchi Ba Zato Ba Tsammani
- Daukewar na'urar sauti ya tilasta kawo karshen gangamin yakin neman zaben APC a jihar Bauchi
- Ana tsaka da taro bayan shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya fara koro jawabinsa sai wuta ya dauke
- Hakan ya tilastawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya halarci gangamin barin wajen tare da mukarrabansa
Punch - Gangamin yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Bauchi ya zo karshe babu zato babu tsammani saboda rashin kyawun na'urar sauti.
Taron wanda ke gudana a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi a ranar Litinin, ya zo karshe bayan wutan lantarki ya dauke kuma an kasa dawo da shi.
Wutan lantarkin ya dauke ne jim kadan bayan shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya hau munbari sannan ya fara gabatar da jawabinsa, jaridar Punch ta rahoto.
Buhari, Tinubu da shugabannin APC sun fice
Nan take shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya halarci gangamin ya bar wajen tare da mukarrabansa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
The Guardian ta rahoto cewa magoya bayan jam’iyyar mai mulki sun bar wajen cikin fushi yayin da Adamu, Tinubu da dan takarar gwamnan jam’iyyar, Sadique Baba Abubakar, suka fice daga inda suka tarar da ayarinsu da ke jira.
Buhari dai ya halarci gangamin ne domin jagoranci wajen yiwa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, yakin neman zabe.
Shugaban kasar ya isa filin jirgin sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi da misalin karfe 10:20am.
Ya samu tarba daga Gwamna Bala Mohammed wanda ya kasance dan takarar gwamna a jam'iyyar Peoples Democratic Party.
APC ta yi babban kamu na mambobin NNPP a jihar Kano
A wani labari na daban, mun ji cewa mambobin jam'iyyar NNPP mai kayan marmari sun sauya sheka daga jam'iyyar ta su Kwankwaso zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kano.
Da suke sanar da sauya shekarsu a wajen gangamin kamfen da ya guda, dandazon masu sauya shekar daga kananan hukumomin Munjibir da Ungogo sun kona jajjayen hulunansu na Kwankwasiyya.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jinjina masu kan wannan mataki da suka dauka yayin da ya gabatar da tutar APC ga yan takara a jihar.
Asali: Legit.ng