Gwamna Wike Ya Fita Daga Harkar Atiku a Ribas, Ya Fito da ‘Dan Takaransa a 2023

Gwamna Wike Ya Fita Daga Harkar Atiku a Ribas, Ya Fito da ‘Dan Takaransa a 2023

  • Alamu na nuna ‘Ya ‘yan jam’iyyar PDP a Ribas su na goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu a 2023
  • Shugaban karamar hukumar Ikwerre, Samuel Nwanosike, ya nuna ba su tare da Atiku Abubakar
  • Hon. Samuel Nwanosike ya ce babu adalci idan har za a sake damka mulki zuwa ga yankin Arewa

Rivers - Jam’iyyar PDP ta reshen jihar Ribas, ta kammala yanke shawarar kin goyon bayan Atiku Abubakar ya zama shugaban Najeriya a 2023.

Wani rahoto da muka samu daga Sun ya tabbatar da cewa alamu sun nuna jam’iyyar PDP ba za ta goyi bayan takarar Atiku Abubakar a Ribas ba.

Abin da ya jawo har aka fahimci wannan shi ne bayani da aka samu daga bakin shugaban karamar hukumar Ikwerre, Hon. Samuel Nwanosike.

Hon. Samuel Nwanosike wanda na hannun daman Gwamna Nyesom Wike ne, ya shaidawa Sunday Sun cewa su na goyon bayan Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

PDP Ta Jawo Danyen Rikici, Gwamna Wike Yana Barazanar Kai Jam’iyyar Zuwa Kotu

Tinubu a maimakon Atiku

A maimakon marawa jam’iyyarsa baya, shugaban karamar hukumar ta Ribas ya ce za su goyi bayan APC da Bola Tinubu a zaben Fubrairun nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Akwai sabani tsakanin ‘dan takaran shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar da gwamnonin PDP da ke G5 wanda Nyesom Wike yake jagoranta.

'Yan PDP
Magoya bayan PDP Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

A cewar Nwanosike, a jihar Ribas, an tsaida matsaya kan ‘dan takararsu na kujerar shugaban kasa.

Wike zai tallata Tinubu?

Binciken da jaridar ta gudanar ya nuna cewa manyan ‘yan gaban goshin Gwamna Wike sun yi taro dabam-dabam kwanan nan a kan batun zabe.

A karshen zaman da aka yi, an cin ma yarjejeniya cewa za a tallata Bola Tinubu a Ribas, kuma shugabannin PDP za su yaki takarar Atiku Abubakar.

Nwanosike ya na zargin cewa shugabannin PDP na kasa sun nuna son kai wajen tafiyar da jam’iyyar, ya ce babu adalci a sake tsaida ‘Dan Arewa.

Kara karanta wannan

Kyau Kwankwaso Ya Hakura – Kungiya ta Kawo Hujjoji Kan Wanda Arewa Za Ta Zaba

Baro-baro, shugaban karamar hukumar Ikwerre ya nuna bayan shekaru takwas, ba za su goyi bayan Muhammadu Buhari ya mika mulki ga Atiku ba.

Wike ya yi aman wuta a PDP

Rahoto ya zo a baya cewa Gwamna Nyesom Wike ya soki dakatarwar da shugabannin jam’iyyar PDP tayi wa wasu shugabanninta a Ekiti.

Mai girma Gwamnan yana ganin an saba doka wajen daukar wannan mataki, zai je kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng