Damammakin da APC, PDP Ke Da Shi a Lagas, Kano Da Wasu Jihohi 3 Mafi Yawan Masu Rijista
Jam'iyyun siyasa da yan takararsu suna ta lissafi don bunkasa damammakin da suke da shi a zaben 2023 wanda ake gab da yi.
Manyan jam'iyyun siyasa da yan takararsu sune Bola Tinubu na All Progressives Congress (APC), Atiku Abubakar na Peoples Democratic Party (PDP), Peter Obi na Labour Party, da Rabiu Kwankwaso na NNPP.
Halin da ake ciki game da Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi, PDP, APC
Yan Najeriya da dama musamman matasa sun jajirce don sauya makomar kasar a zabe mai zuwa yayin da suka yi rijista sosai don kada kuri'a a yayin zabe.
Jihohi mafi yawan masu rijista na iya taka rawar gani sosai kan dan takarar da zai zama magajin shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Mayu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Saboda haka, an lissafo jerin jihohi biyar da ke da mafi yawan masu rijista da kuma damammakin da wadannan jam'iyyun siyasa da yan takararsu ke da shi.
Manyan jihohi 5 da damammakin da APC, PDP da Labour Party ke da shi a cikinsu
Legas, masu rijistan zabe 7,060,195
Jihar Lagas na da kimanin mutum miliyan 20 kuma Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta bayyana cewa fiye da mutum miliyan 7 ne suka yi rijista don kada kuri'a a jihar a zabe mai zuwa.
APC na iya lashe zabe a jihar saboda ganin cewa ta lashe jihar a zabukan 2015 da 2019. Dan takarar shugaban kasar jam'iyyar shine kuma tsohon gwamnan jihar.
Kano, masu rijistan zabe 5,921,370
Jihar ta arewa ita ce ta biyu a yawan masu rijistan zabe a 2023. Fiye da mutum miliyan 5 ne suka yi rijista don zabe a jihar bisa kididdigan hukumar INEC.
Kamar jihar Lagas, ana ganin APC ce za ta lashe jihar itama saboda jam'iyyar ke ta kawo jihar tun 2015 sannan ita ta samar da kuri'u mafi yawa ga shugaba Buhari a zabuka biyu da suka gabata.
Kaduna, masu rijistan zabe 4,335,208
Jihar ce ke bin Kano wajen yawan masu rijista inda take da mutum fiye da miliyan hudu.
Bola Tinubu na APC na iya lashe jihar a zabe mai zuwa kasancewar gwamnan ya sha nuna cewa jam'iyya mai mulki ta fi kowa dama a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Rivers, masu rijistan zabe 3,537,190
Jihar na daya daga cikin jihohi mafi zafi a zabe mai zuwa da masu rijistan zabe miliyan 3.5 sabanin miliyan 3.21 da aka samu a 2019.
Atiku Abubakar na PDP na iya kawo jihar duk da rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar wanda ya haddasa gaba tsakaninsa da Gwamna Nyesom Wike.
Katsina, masu rijistan zabe 3,516,719
Katsina ce jiha ta biyar a masu yawan kuri'u a zaben 2023. Yanzu haka, fiye da mutum miliyan 3.5 ne suka yi rijista a zabe mai zuwa.
Duk da matsalolin rashin tsaro a jihar, kasancewar shugaban kasa Buhari dan jihar ya sake ba APC damar kasancewa a saman sauran jam'iyyun siyasa a jihar.
Asali: Legit.ng