Bauchi Da Wata Jaha 1 da APC Ke Shirin Kwacewa Daga Hannun PDP a Zaben 2023
- Dabarar kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC na tabbatar da ganin Buhari ya halarci gangamin jam'iyyar a jihohin PDP 2 a watan nan ya nuna muhummancin jihohin
- Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasar, ya bayyana a makon jiya cewa shugaban kasar zai yi wa jam'iyyar kamfen a jihohi 8 tsakananin 23 ga watan Janairu da 21 ga watan Fabrairu
- Akwai jihohin PDP 2 da suka samu shiga jerin kuma suna da karfin tattalin arziki saboda jihohi ne masu albarkatun man fetur
Jam'iyyun siyasa na ta yin martani da kokarin ganin nasara ya zo bangarensu yayin da ake ci gaba da yakin neman zaben 2023 cike da dabaru.
Sai dai kuma, jam'iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) na ta shirya dabarun cin galaba kan juna kasancewarsu jam'iyya mai mulki da babbar mai adawa a kasar.
Jihohin PDP da APC ke zawarci a zaben 2023
Shakka babu jam'iyyar APC na yunkurin ganin ta kwato wasu manyan jihohi biyu da PDP ke jan ragamarsu a babban zabe mai zuwa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A ranar Asabar, 14 ga watan Janairu, Bashir Ahmad, mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara ta musamman a kafofin sadarwar zamani, ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa shugaban kasar zai yi kamfen din shugaban kasa na APC a jihohi takwas.
Manyan jihohi biyu da ke cikin jerin suna karkashin ikon PDP ne. Sune:
- Bauchi
- Akwa Ibom
Jihohin biyu sun kasance masu karfin tattalin arziki domin dai suna samar da man fetur.
Koda dai Bauchi jihar arewa ce yayin da Akwa Ibom ta kasance a kudu maso kudu, jihar ta arewa na daya daga cikin jihohin arewa biyu da aka fara hakar mai a kwanan nan, karfin tattalin arzikinta zai zama mai matukar amfani ga jam'iyyar APC mai mulki.
An shirya dabaru a yakin neman zaben shugaban kasa na APC a 2023 domin dai shugaban kasar ya hallara ne kawai a gangamin yakin neman zaben jam'iyyar na Jos da Adamawa.
Gangamin na Jos da shine aka bude kamfen din yayin da watakila shugaban kasar ya hallara a Adamawa ne saboda jam'iyyar ta gabatar da yan takara mace, Aishatu Binani.
Binani na takara don tsige Ahmadu Fintiri, dan takarar PDP mai ci wanda ke neman zarcewa a karo na biyu kuma jihar ita ce mahaifar Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP.
Kalli wallafar Bashir:
Dan takarar gwamnan APC a Bauchi bai samu karbuwa a wajen mutanensa ba
A wani labarin kuma, mun ji cewa al'ummar mahaifar dan takarar gwamnan APC a jihar Bauchi, Abubakar Sadiqque sun yi fatali da shi inda suka rungumi jam'iyyar PDP ta Bala Mohammed.
Daruruwan mambobin APC da suka koma PDP sun ce makiyan jihar Bauchi ne kadai za su zabi dan takarar tsohuwar jam'iyyarsu domin a cewarsu, babu abun da zai tsinana.
Asali: Legit.ng