Ba Jam'iyyar Da Dawo Da Zaman Lafiya a Jihar Neja Banda PDP, Atiku
- Mai neman zama shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya nemo wa yan Najeriya maganin matsalar tsaro
- A wurin ralin neman zabensa na jihar Neja, Atiku ya yi ikirarin cewa ba jam'iyyar da zata iya dawo da zama lafiya banda PDP
- Neja na daya daga cikin jihohin arewa ta tsakiya da ke fama da matsalar hare-haren 'yan bindiga
Niger - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce jam'iyyarsa ce kaɗai zata iya dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Neja.
The Cable ta rahoto cewa Atiku ya bayyana haka ne ranar Asabar a wurin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa da ya gudana a Minna, babban birnin jihar.
A watannin da suka gabata, Neja dake arewa ta tsakiya ta shaida hare-haren 'yan bindigan daji, waɗanda ke garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, wasu lokutan su kashe wanda suka sace.
Tsohon mataimakin shugaban kasan yace lokacin da PDP take kan madafun iko, jihar Neja ba ta san wani abu mai suna harin ta'addanci ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Atiku ya ce:
"Da farko muna gode muku bisa taruwarku a nan da kuma goyon bayan da kuke nuna mana tun da muka sa ƙafa a Neja."
"Allah ya dawo da zaman lafiya a Neja, wanda kun san idan aka cire PDP babu jam'iyar da zata dawo maku da zaman lafiya. Lokacin da PDP ke kan mulki 1999-2015 shin akwai matsalar tsaro a Neja?"
"Saboda haka muna tabbatar maku da cewa idan kuka zabi PDP ta hau mulki a Neja, rashin tsaro zai zama tarihi idan Allah ya so. Haka batun gina tashar Jirgin ruwa a Baro, PDP ta fara kuka ce canji, yanzu kun ga canji."
Ina rokon ku PDP ta koma mulki - Atiku
Wazirin Adamawa ya kara da miƙa roko ga dandazon mahalarta ralin, inda ya nemi su zabi jam'iyyar PDP ta koma kan gadon mulki a zabe mai zuwa.
Tribune ta rahoto Atiku na cewa:
"Me canjin ya kawo muku? Rashin tsaro, wahala da karayar tattalin arziki. Muna roƙon ku zabi PDP ta dawo da tsaro a Neja da sauran sassan kasar nan."
A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Yi Barazanar Soke Wurin da Atiku Zai Yi Kamfe a jihar Ribas
Gwamnan jihar Ribas kuma jagoran gwamnonin G-5, Nyeson Wike, ya gargadi kwanitin kamfen Atiku ya nesanta kansa da filin wasan Adokiye Amiesimaka.
A cewar gwamnam duk da gwamnatinsa ta amince Atiku ya yi kamfe a wurin, ba zata yarda wani ya fara nuna iko da filin ba wata ɗaya kafin ranar taron.
Asali: Legit.ng