Kotu Ta Kori Dan Takarar Majalisar Tarayya Na PDP a Jihar Imo

Kotu Ta Kori Dan Takarar Majalisar Tarayya Na PDP a Jihar Imo

  • Yayin da ya rage kwanaki 35 babban zabe, Kotu mai zama a Abuja ta jika wa jam'iyyar PDP a aiki a jihar Imo
  • A ranar Jumu'a babbar Kotun tarayya ta kori ɗan takarar PDP daga neman mamban majalisar wakilai mai wakiltar Aboh Mbaise/Ngor Okpala
  • Alkalin Kotun ya baiwa jam'iyyar PDP wa'adin mako biyu ta sauya sabon zaben fidda gwani a mazaɓar

Abuja - Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta soke tikitin dan takarar jam'iyyar PDP na mazabar mamban majalisar wakilai mai wakiltar Abor Mbaise/Ngor Okpala, jihar Imo, Albert Agulanna.

Yayin yanke hukunci kan ƙarar da Uzoma Ugochukwu ya shigar gabanta, Kotun a ranar Jumu'a ta umarci jam'iyyar PDP ta sake sabon zaben fidda gwani a mazabar cikin kwanaki 14.

Gudumar Kotu.
Kotu Ta Kori Dan Takarar Majalisar Tarayya Na PDP a Jihar Imo Hoto: punchng
Asali: UGC

Jaridar Punch ta tattaro cewa Mazaɓar Aboh Mbaise/Ngor Okpala nan ne mazaɓar tsohon gwamnan jihar Imo wanda ya gabata watau Emeka Ihedioha.

Kara karanta wannan

NNPP Ta Ruɓe, An Bayyana Wanda Ya Kamata Kwankwaso Ya Janye Wa Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

Wannan ci gaban na zuwa ne kasa da mako ɗaya bayan Kotun koli ta soke tikin dan takarar Sanatan Imo ta yamma a inuwar PDP, Jones Onyereri, a cewar rahoton The Nation.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ana zargin tsohon gwamna Ihedioha da kulla makircin da ya haddasa korar dan takarar Sanata, Mista Onyereri, haka kuma ana ganin Sakataren PDP na kasa, Samuel Anyanwu, ne ya jawo Kotu ta kori Agulanna.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa Ihedioha da Anyanwu sun numa sha'awar tikitin takarar gwamnan jihar Imo a inuwar jam'iyyar PDP.

Haka nan alamu sun nuna da yawan mambobin jam'iyyar PDP a jihar sun shiga damuwa kan rigingimun da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa a cikin jam'iyya.

Amma mai magana da yawun PDP a jihar Imo, Collins Opuruozor, ya ce:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku Abubakar Ya Dira Jihar Matashin Gwamnan G-5, Ya Shiga Matsala Tun a Filin Jirgi

"Maƙiyan jam'iyyar PDP wadan da gabansu ya fadi sakamakon ganin yadda mutane suka amince da ita ne suke amfani da Kotu domin fidda PDP daga shiga zaɓe."

Wike ya gargaɗi PCC-PDP kan wurin kamfe

A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Yi Barazanar Soke Wurin da Atiku Zai Yi Kamfe a jihar Ribas

Gwamnan jihar Ribas kuma jagoran gwamnonin G-5, Nyeson Wike, ya gargadi kwanitin kamfen Atiku ya nesanta kansa da filin wasan Adokiye Amiesimaka.

A cewar gwamnam duk da gwamnatinsa ta amince Atiku ya yi kamfe a wurin, ba zata yarda wani ya fara nuna iko da filin ba wata ɗaya kafin ranar taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262