'Dan Takarar Gwamnan Jigawa a Jam'iyyar LP, Ya Sauya Sheka Zuwa APC
- 'Dan takarar gwamnan jihar Jigawa a karkashin jam'iyyar Labour Party, Yusuf Tsoho, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
- Gwamna Muhammad Badaru na jihar ne ya karba Tsoho a hukumance zuwa APC a gidan gwamnatin jihar ranar Juma'a
- Kamar yadda mai magana da yawun gwamnan ya sanar, Tsoho da magoya bayansa zasu samu dama kamar tsofaffin 'yan jam'iyyar
Jigawa - Yusuf Tsoho, 'dan takarar gwamna a jam'iyyar Labour Party a jihar Jigawa, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar, jaridar TheCable ta rahoto.
A wata takarda ta ranar Juma'a, Habiba Nuhu Kila, mai bada shawa kan yada labarai ga Muhammad Barau Abubakar, gwamnan jihar Jigawa, yace ubangidansa a hukumance ya karba Tsoho zuwa jam'iyyar a gidan gwamnatin jihar da ke Dutse.
Channels TV ta rahoto cewa, mai bada shawara ga gwamnan ya yanko Abubakar na cewa, Tsoho da magoya bayansa za a basu duk wata dama da tsoffin 'yan jam'iyyar ke da ita a jihar.
Kila yace Tsoho ya kwatanta nagartar APC kan yadda ta magance matsalolin masu zabe a jihar a matsayin dalilinsa na komawa jam'iyyar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A daya bangaren, Abubakar Marke, 'dan takarar mazabar Kaugama a karkashin jam'iyyar PDP na majalisar jihar Jigawa ya koma jam'iyyar APC.
Auwal Sankara, kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Jigawa, ya sanar da wanann cigaban a wata takardar da ya fitar ranar Juma'a.
Sankara yace Marke ya yanke hukuncinsa na komawa jam'iyyar APC bayan ganawa da yayi da gwamnan jihar.
'Yan jam'iyyar APC 8 sun rasu a hatsarin mota a Zamfara
A wani labari na daban, magoya bayan Gwamna Muhammad Bello Matawallen Maradun a jihar Zamfara sun tafka hatsarin mota inda wasu takwas daga ciki suka koma ga Allah.
Hatsarin ya auku a ranar Alhamis a kan titin Gummi zuwa Bukkuyum inda suka dawo daga kamfen din gwamnan.
Tuni aka yi jana'izarsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a ranar Juma'a inda Gwamnan tare da tawagarsa suka samu halarta.
Sun garzaya fadar Sarkin Bukkuyum din inda suka yi masa ta'aziyya tare da jama'ar jihar baki daya kan wannan rashin.
Asali: Legit.ng