2023: Wamakko, Dingyadi Za Su Jagoranci Mambobi 369 Na Kwamitin Yakin Neman Zaben APC a Sokoto

2023: Wamakko, Dingyadi Za Su Jagoranci Mambobi 369 Na Kwamitin Yakin Neman Zaben APC a Sokoto

  • An kaddamar da kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar APC a jihar Sokoto a ranar Alhamis, 19 ga watan Janairu
  • Sanata Aliyu Wammakko da Maigari Dingyadi ne za su jagoranci kwamitin mai mambobi 369
  • A wata mai kamawa ne za a gudanar da babban zaben shugaban kasar Najeriya

Sokoto - Sanata Aliyu Wammakko mai wakiltan Sokoto ta arewa a majalisar dokokin tarayya da Ministan harkokin yan sanda, Alhaji Maigari Dingyadi, za su jagoranci kwamitin yakin neman zaben APC mai mambobi 369 a jihar Sokoto.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa wannan ci gaban ya biyo bayan rantsar da kwamitin a Sokoto a ranar Alhamis, 19 ga watan Janairu.

Wamakko
2023: Wamakko, Dingyadi Za Su Jagoranci Mambobi 369 Na Kwamitin Yakin Neman Zaben APC a Sokoto Hoto: PM News
Asali: UGC

PM News ta rahoto cewa Wamakko wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar kuma shugaban APC a jihar shine shugaban kwamitin yayin da Dingyadi ya kasance Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku Abubakar Ya Dira Jihar Matashin Gwamnan G-5, Ya Shiga Matsala Tun a Filin Jirgi

Wasu daga cikin mambobin kwamitin

Wasu daga cikin manyan shahararrun mambobin kwamitin sun hada da Alhaji Ahmed Aliyu, dan takarar gwamnan APC, Sanata Ibrahim Gobir, dan majalisa mai wakiltan Sokoto ta gabas a majalisar dokokin kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai kuma Sanata Ibrahim Danbaba, dan majalisa mai wakiltan Sokoto ta kudu a majalisar dokokin tarayya da kuma Alhaji Chiso Dattijo, kwamishin hukumar kidaya ta kasa.

Cikin wadanda suka samu shiga jerin harda Alhaji Idris Danchadi, abokin tafiyar dan takarar gwamna, Abdullahi Tafida, Amb. Sahabi Gada, Amb. Abubakar Wurno da Muhammadu Sifawa.

A jawabinsa, Wamakko ya jinjinawa mutanen jihar kan soyayyar da suke nuna masa da APC, rahoton PM News.

Ya ce:

"Ba zan iya gode maku ba a kan sadaukarwa da jajircewarku ga manufofin jam'iyyarmu wacce ke da nufin kawo jagoranci mai ma'ana a Sokoto da Najeriya."

Kara karanta wannan

Wike Ya Samu Tangarɗa, Gwamnan G-5 Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Yuwuwar Haɗewa da Atiku

APC ta rasa babban mai daukar nauyinta da dubban mabiyansa a jihar Delta

A wani labari na daban, wani jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta rasa daya daga cikin manyan jiga-jiganta a yankin Ndokwa da ke jihar Delta, Cif Tony Amechi, inda ya fice zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Amechi ya fice daga jam'iyya mai mulki ne tare da dubban mabiyansa. Ya yi ikirarin cewa jam’iyyar bata nufin mutane da alkhairi saboda haka ba zai dauki nauyinta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng