Sarkin Musulmi Ya Faɗi Wanda Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Zaba a 2023

Sarkin Musulmi Ya Faɗi Wanda Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Zaba a 2023

  • Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana wa yan Najeriya shugabannin da ya kamata su jefa wa kuri'unsu a 2023
  • Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce Najeriya ta yi wa kasashe da yawa nisa game da tsaro don haka ya kamata mutane su rika alfahari da kasarsu
  • Sarkin ya bayyana cewa lokaci ya yi da yan Najeriya zasu jingine batun kabilanci yayin zaben shugabanni

Sokoto- Sarkin Musulmai kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya shawarci 'yan Najeriya game da zaben 2023.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Sarkin Musulmi ya bukaci 'yan Najeriya su natsu a zabi mai zuwa, su zaɓi shugabanni masu kyawawan halaye.

Sarkin Musulmi.
Sarkin Musulmi Ya Faɗi Wanda Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Zaba a 2023 Hoto: Sultan Alhaji Sa’ad Abubakar III.
Asali: UGC

Sultan ya yi wannan kira ne ranar Alhamis yayin da yake jawabi ga mahalarta taron majalisar kula da albarkatun ruwa ta kasa (NCWR) a jihar Sakkwato.

Kara karanta wannan

2023: Mutane Za Su Yi Alfahari da Kasancewarsu Yan Najeriya Idan Na Gaje Buhari, Peter Obi

Sarkin Musulmin ya bayyana cewa babban zaɓe na ƙara matsowa kuma 'yan Najeriya na bukatar su sa wayewa da basira wajen amfani da kuri'unsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Yan Najeriya na bukatar su yi tunani su ƙara nazari kan nazari kan wanda zasu jefa wa kuri'unsu, bai kamata mu duba Addini ko kabilanci kan kowaye zamu zaba ba, kishin Najeriya ne a farko."
"Kasar mu ya kamata mu fifita a saman komai kuma kar mu sake mu zabi mutumin da zai ƙara lalata yanayin da muke fama a yanzu."

Mai Alfarma Sarkin Musulmin ya ƙara da cewa idan har ana son Najeriya ta ci gaba, ya zama wajibi 'yan kasa sun jingine batun Ƙabilanci a fuskanci zahiri.

Sarkin ya ci gaba da cewa:

"Ƙasar mu tayi wa wasu kasashe da dama nisa a bangaren tsaro saboda haka ya kamata mu cigaba da goyon baya da yabon ƙasarmu da shugabanninmu domin su samu karsashin magance ƙalubalenmu."

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tono Asalin Matsala, Ya Fadi Abu Ɗaya Tak Da Ya Kawo Yan Bindiga Arewacin Najeirya

Bayan haka Sultan ya gode wa gwamnatin tarayya, ministan albarkatun ruwa da sauran jami'an ma'aikatarsa bisa kawo taronsu jihar Sakkwato, NAN ta ruwaito.

Ka sulhunta da su Wike - Olubadan

A wani labarin kumakuma Sarkin kasar Ibadan ya bukaci Atiku ya gaggauta rarrashin G5 idan har dagaske yana son kai labari a 2023

Babbar basakaren Ibadanland, Oba Lekan Balogun, ya roki Atiku ya sulhunta da gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da sauran gwamnonin G5 tun da wuri.

Basaraken, wanda ya kira Atiku da abokinsa, ya nemi a Atiku ya duba matsayin sarakuna a Najeriya idan ya zama shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262