Akwai Ƙura: “Ba a Gina Makarantar da Tinubu Yake Ikirarin Ya Yi Karatun Boko ba”
- Incorporated Trustees of Advocacy for Social Right Advancement & Development Initiative ta koma kotu
- Kungiyar nan mai zaman kan ta, tana so kotun tarayya mai zama a Abuja ta binciki ‘dan takaran APC
- Ana zargin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bai yi karatu a makarantar firamaren da yake ikirarin ya yi ba
Abuja - Wata kungiya mai zaman kanta, ta ce je kotu tana cewa Duniya ta san da zaman makarantar da Bola Ahmed Tinubu ya ce ya yi firamare ba.
Punch ta ce an shigar da kara ne a gaban Mai shari’a Mobolaji Olajuwon na kotun tarayya a Abuja.
Kungiyar Incorporated Trustees of Advocacy for Social Right Advancement & Development Initiative tana zargin ‘dan takaran ya yi karyar karatu.
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana ikirarin ya yi firamarensa a makarantar St. Paul Aroloya a Legas, kungiyar tace ba a yi makarantar a lokacinsa ba.
A dalilin wannan zargi, kungiyar ASRADI ta shigar da karar ‘dan takaran na shugaban kasa, tana neman a bincike shi bisa karya kan rantsuwa.
ASRADI ta ce bayanan da ta samu daga takardar CF 001 da Bola Tinubu ya gabatarwa hukumar zabe na INEC, ya nuna ‘dan takaran ya na karyar ilminsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da zai shiga takarar Gwamnan jihar Legas a zaben 1999, Tinubu ya jero St. Paul Aroloya da Children Home School a cikin makarantun da ya halarta.
Karar da kungiyar take yi shi ne ‘yan sanda su binciki ikirarin ‘dan takaran domin a shekarar da yake magana, ba a gina wannan makaranta a ko ina ba.
Aikin 'yan sanda ne su binciki Tinubu
Masu karar sun ce nauyi ya rataya a kan hukuma su binciki zargin da ake yi wa ‘dan siyasar mai neman zama shugaban kasar Najeriya a zabe mai zuwa.
ASRADI ta ce a dalilin kin yin abin da ya dace daga bangaren ‘yan sanda, tsohon Gwamnan na Legas yana yawo hankali kwance, har ya shiga takara.
This Day ta rahoto cewa wannan kungiya ta dogara ne da sashe na 215(1) (a) na tsarin mulki da sashe na 7(1), 31 da 32 na dokar aikin ‘yan sandan Najeriya.
Idan aka yi la’akari da abin da dokar kasa ta ce, wajibi ne a kan jami’an ‘yan sandan Najeriya su binciki wannan zargi na yi wa hukuma karya da rantsuwa.
'Sharrin' Abba Kyari a kan Bukola Saraki
An samu rahoto Ayoade Akinnibosun wanda ake zargi da fashin banki ya ce an yi masa tayin miliyoyi da biza domin ya yi wa Dr. Bukola Saraki kazafi.
A cewar Akinnibosun DCP Abba Kyari ya ce ya amsa cewa Bukola Saraki ne ya tura su yin fashi, idan ya yi haka zai samu N10m da damar fita kasar waje.
Asali: Legit.ng