Kano 2023: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya Tsakanin Yan Takarar Gwamna

Kano 2023: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya Tsakanin Yan Takarar Gwamna

  • Gabannin babban zaben 2023, yan takarar kujerar gwamnan jihar Kano sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya
  • Yan takara daga fadin jam'iyyun siyasa daban-daban sun kulla yarjejeniyar yin zaben 2023 cikin lumana a jihar Kano
  • A yayin taron da ya gudana a yau Laraba, 18 ga watan Janairu, fadakar da yan takara kan muhimmancin zaman lafiya kafin zabe, lokacin zabe da kuma bayan zabe

Yan makonni kafin babban zaben 2023, yan takarkar kujerar gwamna a jihar Kano sun sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Sanya hannun da yan takarar suka yi, ya biyo bayan gayyatar da kwamitin tabbatar da zaman lafiya ta jihar Kano wato KPC da hadin gwiwar Cibiyar Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa suka yi masu.

Yan takarar gwamnan Kano
Kano 2023: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya Tsakanin Yan Takarar Gwamna Hoto: Aminiya
Asali: UGC

Sun rattaba hannun ne a wajen wani taron fadakar da yan takara kan muhimmancin zaman lafiya kafin, lokaci da kuma bayan zabe wanda aka yi a ranar Laraba, 18 ga watan Janairu, rahoton Aminiya.

Kara karanta wannan

Hotunan Shugaba Buhari Inda Ya Samu Lambar Yabon Wanzar da Zaman Lafiya a Afrika

Kwamitin ya kuma nusar da matasa da ke amfani da kafafen sadarwar zamani da su zamo masu yada abubuwan da zai amfani al'umma da wanzar da zaman lafiya a fadin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin yan takarar da suka kulla yarjejeniyar zaman lafiya a Kano

Yan takarar da suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya ta zaman lafiya sun hada da Salihu Tanko Yakasai na Jam’iyar PRP, Sha’aban Ibrahim Sharada na Jam’iyar ADP da Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-gida na Jam’iyar NNPP.

Sauran sune mataimakin dan takarar gwamna na Jam’iyar APC, Murtala Sule Garo, Bashir I. Bashir na Jam’iyar LP, Muhammad Abacha na Jam’iyar PDP, Mallam Ibrahim Khalil na Jam’iyyar ADC ya wakilce sa, sai kuma Bala Gwagwarwa na Jam’iyar SDP.

Giovanie Biha, wakiliyar Majilisar Dinkin Duniya fa Afirka ta ja hankalin yan takarar da su tabbatar da an gudabar da zabe a cikin kwanciyar hankali da lumana.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Daya Daga Cikin Gwamnonin G-5 Ya Sauya Tunani, Zai Hade da Atiku Abubakar

Tun farko dai shugaban sakatariyar kwamitin zaman lafiyan, Ambasada Ibrahim A. Waiya, ya ce sun taba shirya irin wannan taro na kulla yarjejeniyar zaman lafiya a jihar Kano tare da hadin gwiwar kwamitin zaman lafiya na kasa kafin zaben 2019, rahoton Leadership.

Shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa, Janar Abdulssalami Abubakar ne ya jagoranci sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiyan.

A wani labari na daban, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi ya sha alwashin inganta tsaro tare da hada kan al'ummar Najeriya idan ya lashe zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel