2023: Za Mu Gina Kasa da Kowa Zai Yi Alfahari da Ita, Inji Obi

2023: Za Mu Gina Kasa da Kowa Zai Yi Alfahari da Ita, Inji Obi

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya ce zai inganta tsaro da bunkasa harkar noma idan ya gaje Buhari a 2023
  • Peter Obi ya ce yan Najeriya za su yi alfahari da kasancewar yan kasar nan idan ya zama shugaban kasa domin akwai tanadi na musamman da ya yi masu
  • Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya daura alhakin kalubalen tsaro a kasar kan rashin shugabanci nagari

Kaduna - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya ce idan aka zabe shi, gwamnatinsa za ta gina kasa da kowa zai yi alfahari da ita, rahoton Punch.

Da yake jawabi a Kaduna a wajen kaddamar da yakin neman zabensa a yankin arewa maso yamma a ranar Laraba, Obi ya cfe zai hada kan Najeriya sannan ya kare ta idan ya zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Manyan Kura-Kurai Aka Tafka, Rashin Shugabanci Na Kwarai a Kasar Nan na Shekaru 24 ne ya Tsundumata Halin da Muke Ciki

Peter Obi
2023: Za Mu Gina Kasa da Kowa Zai Yi Alfahari da Ita, Inji Obi Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Rashin shugabanci nagari ke kawo matsalar tsaro, Obi

Dan takarar na LP ya daura alhakin rashin tsaro a kasar kan shugabanci mara kyau, jaridar TheCable ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Obi ya ce:

"Lamarin tsaro ba wai saboda yan bindiga da sauran miyagu sun fi gwamnati karfi bane, ya kasance ne saboda rashin shugabanci nagari. Wannan ne dalilin da yasa yan bindiga suka mamaye koina suna aiki hankali kwance, suna kashe mutane da lalata dukiyoyi.
"Za mu sauya fasalin tsarin tsaro. Za a kula da jami'an tsaro. Za mu tabbatar da ganin an kula da rayuwarsu don a kula da iyalansu a yanayin da waninsu ya mutu.
"Ni da Datti za mu sauya kasar nan daga mai lakume abinci zuwa mai samar da abinci, saboda tsadar abubuwa. Dukkanin yalwatattun filayen da ke arewa za su zama cibiyar noma. Jihar Kaduna za ta sake zama cibiyar sarrafa albarkatun noma.

Kara karanta wannan

Dino Malaye Yace Ta Karewa Tinubu A Yankinsa Na Kudu Maso Yamma, Tunda Shugabannin Yankin Basa Yinsa

"Bankin noma za ta dauki nauyin samar da abinci a Najeriya da bayar da tallafi ga kungiyoyin matasa, mata da daukacin yan Najeriya - kokarinsu ga jam'iyyar ba zai tafi a banza ba.
"Mu na kokarin dawo da Najeriya inda kowa zai yi farin cikin kasancewa a cikinta. Jihar Kaduna ta wakilci samar da abubuwa a arewa. Ta wakilci abun da ke da kyau a Najeriya. Kuma wannan shine abun da muke so mu dawo da shi. Mun gaji da jin tatsuniyoyi.
"A jihar Kaduna ne sansanin soji mafi kyau a kasar yake. Ya kamata ta kasance da tsaro fiye da sauran yankunan kasar, amma akwai matsalolin tsaro da yawa a jihar.
"Za mu kare sannan mu sake hada kan Najeriya. Tsaro zai sake dawowa."

Ba na ganin Peter Obi zai kai labari a 2023, Bashir Ahmad

A wani labarin, mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan kafofin sadarwar zamani, Bashir Ahmad, ya ce bai ga alamar dan Peter Obi zai lashe zaben shugaban kasa a 2023 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng