Dubbannin Mambobin APC Sun Koma PDP a Jihar Shugaba Buhari
- Jam'iyyar APC ta yi babban rashi yayin da dubbannin mambobinta suka sauya sheka zuwa PDP a karamar hukumar Ingawa
- An samu wannan ci gaban ne lokacin da jirgin yakin neman zaben Atiku/Lado ya dira yankin a jihar Katsina
- Dan takarar gwamna a inuwar PDP, Sanata Dan-Marke, ya dauki alƙawarin samar da walwala da jin dadi ga Katsinawa
Katsina - Dubbannin mambobin All Progressives Congress (APC) sun sauya tunani sun koma jam'iyyar PDP a karamar hukumar Ingawa ta jihar Katsina.
Channels tv tace hakan ya faru ne yayin da tawagar yakin neman zaben ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, Yakubu Lado Danmarke, suka gudanar da Rali a yankin.
Shugaban PDP reshen jihar Katsina, Lawal Magaji Danbaci, shi ne ya bayyana haka wurin Ralin wanda ya samu halartar dubun dubatar magoya bayan PDP.
Shugaban ya yi bayanin cewa daruruwan 'yan siyasan sun ce lalacewar abubuwa da tsadar rayuwa a mulkin APC ne ya sa suka tattara domin neman mafita suka koma PDP.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yakubu Lado ya dauki alkawurra a Ingawa
A wurin kamfen, Dan takarar gwamnan Katsina a PDP ya koka kan yadda rayuwa ta kara wahala musamman yawaitar yunwa da Talauci a shekaru Bakwai da rabu da suka shude.
Yakubu Lado ya yi alkawarin samar da ruwa domin habaka noman rani, tabbatar da wadatar abinci, samar da taki ga manoma a farashi mai rahusa da kuma jawo kowa a jiki.
Ya ce:
"Daga alamun da nake iya fahimta a fuskokinku yau, na damu matuka ganin yadda kuke cikin yunwa da rama idan aka kwatanta shekarar 2015."
"Mun yi matukar farin ciki da karamcinku ta yadda kuka hito kuka tarbe mu maza da mata da kananan yara."
Danmarke ya kara da cewa idan har aka zabe shi a 2023, zai samar da ayyukan yi ga matasa, ya gina tattalin arziki mai karfi sannan kuma ya inganta bangaren lafiya, noma da da Ilimi a jihar Katsina.
A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Yi Sabbin Nade-Nade 7 a Hukumar Yaki Da Rashawa Ta kasa ICPC
Watanni gabanin ya sauka, Shugaba Buhari ya amince da sabunta naɗin kwamishinonin hukumar ICPC ta ƙasa.
Shugaban kasa Buhari ya bi umarnin kundin mulki. ya aike da sunayen mutanen ga majalisar dattawan Najeriya domin ta tantance su.
Asali: Legit.ng