Shugaba Buhari Ya Yi Sabbin Nade-Nade 7 a Hukumar Yaki Da Rashawa

Shugaba Buhari Ya Yi Sabbin Nade-Nade 7 a Hukumar Yaki Da Rashawa

  • Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amince da sabunta naɗin kwamishinonin hukumar ICPC guda 7
  • Shugaban ya aike da sunayen mutane 7 da yake son sake maida wa matsayin su ga majalisar dattawan Najeriya domin tantancewa
  • A ranar 29 ga watan Mayu, 2023 ne wa'adin Buhari zai kare ya miƙa wa wanda yan Najeriya suka zaba a watan Fabrairu

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nemi amincewar majalisar Dattawa na sake naɗa mutane 7 a matsayin kwamishinonin hukumar yaki da rashawa ta ƙasa (ICPC).

Shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar shugaban kasa a zauren majalisar ranar Talata, 17 ga watan Janairu, 2023.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Shugaba Buhari Ya Yi Sabbin Nade-Nade 7 a Hukumar Yaki Da Rashawa Hoto: Presidency
Asali: Instagram

A rahoton jaridar This Day, an tattaro Sanata Ahmad Lawan na karanta wasikar da cewa:

"Dogaro na sashi na 3 (3) da (7) na kunshin dokokin hukumar ICPC 2000, na rubuta wasikar neman sahalewar Sanatoci domin sake naɗa jerin sunayen mutane 7 da zan ambata a ƙasa."

Kara karanta wannan

Atiku Ya Tona Asirin Manyan Yan Takara Biyu, Yace Hatsari Ne Babba a Zabe Su a 2023

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina neman majalisa ta amince su koma matsayinsu na kwamishinonin hukumar Independent Corrupt Practices and other Related Offences Commission (ICPC)."

Jerin sunayen mutane 7 da Buhari ya tura majalisar dattawa

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa sunayen mutanen da Buhari ya nemi sake maida wa matsayin kwamishinoni a hukumar ICPC sun haɗa da, Mai Shari'a Adamu Bello (mai ritaya) daga jihar Katsina.

Sauran su kunshi, Hannatu Muhammed, daga jihar Jigawa, Mista Olubukola Balogun daga jihar Legas, Dakta Grace Nkechiyere Chinda daga jihar Delta da Mista Obiora Samuel Igwedibia daga Anambra.

Ragowar mutane biyun su ne, Abdullahi Maikano, daga jihar Neja, arewa ta tsakiya da kuma Dauda Yahaya Umar dan asalin jihar Nasarawa a Najeriya, kamar yadda jaridar Guardian ta rahoto.

Wannan naɗin na shugaban kasa na zuwa ne yayin da ya rage 'yan watanni ya sauka daga kan gadon mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Kara karanta wannan

Da Dumi-duminsa: Shahararren Jarumin Nollywood Papa Ajasco Ya Rasu

A wani labarin kuma kun ji cewa Shugaban kasar Najeriya zai kai ziyarar kwana biyu kasar Larabawa ta Mauritania

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaban kasan zai halarci taron zaman lafiya a kasar kuma ana sa ran zai yi jawabi ga mahalarta taron.

A cewar mai magana da yawun shugaban ƙasa, Femi Adesina, za'a baiwa Buhari lambar yabo a wurin taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262