Shugaba Buhari Zai Shilla Kasar Mauritania Ranar Litinin

Shugaba Buhari Zai Shilla Kasar Mauritania Ranar Litinin

  • Shugaban kasar Najeriya zai kai ziyarar kwana biyu kasar Larabawa ta Mauritania don taron zaman lafiya
  • Shugaba Muhammadu Buhari zai samu lambar yabon jagoran tabbatar da zaman lafiya a taron
  • Wannan ba shine karo na farko da Shugaban kasan zai ziyarci kasar ta Mauritania ba

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin zai yi tafiya Nouakchott, babbar birnin jamhuriyyar Musuluncin Mauritania domin halartan taron shugabannin kasar Afrika kan zaman lafiya.

Wannan shine karo na uku da wannan taro zai gudana.

Shugaba Buhari zai gabatar da jawabi a wajen taron kan nasarorin da aka samu wajen samar da zaman lafiya a Afrika.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Lahadi.

Buhari
Shugaba Buhari Zai Shilla Kasar Mauritania Ranar Litinin Hoto: Presidency

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Zan Bayar Da Ilimi Kyauta Idan Na Zama Gwamnan Kano - Abba Gida-gida

Ya ce a wajen taron za'a baiwa Shugaba Buhari kyautar lambar yabon "Mai Karfafa Zaman Lafiya A Afrika".

A cewarsa, za'a bashi wannan lambar yabo ne bisa jagorancin da ya nuna wajen wanzar da zaman lafiya a nahiyar ta hanyar gudunmuwa da sulhun da taimakawa da shi.

Femi Adesina ya ce cibiyar zaman lafiyan Abu Dhabi ce zata gabatar da wannan lambar yabo.#

A wani sashen na jawabin yace:

"Gabanin bashi lambar yabon tabbatar da zaman lafiya a Afrika, Shugaban kasa zai halarci taron zaman lafiyan Afrika karo na uku inda zai gabatar da jawabi kan nasarorin da aka samu wajen saman da zaman lafiya a Afrika."
"Shugaban kasan zai tafi Nouakchott ranar Litinin sannan ya dawo ranar Laraba kuma zai samu rakiyar Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; ministan tsaro, Maj. Gen. Bashir Salihi Magashi; NSA Babagana Munguno da Dirakta janar na NIA, Amb. Ahmed Rufai Abubakar.”

Shugaba Buhari Ya Halarci Bikin Ranar Sojoji Da Ya Gudana a Abuja

Kara karanta wannan

Bidiyon Shugaba Buhari Yayin da Ya Isa Filin Taron Bikin Ranar Sojoji

A wani labarin kuwa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci taron ranar tunawa da jaruman sojin Najeriya da suka mutu a filin daga .

Taro na shekarar 2023 ya gudana ne a babban birnin tarayya Abuja ranar Asabar, 15 ga watan Junairu, 2023.

Da isar shugaba Buhari filin taron da misalin karfe 10:05 na safe, sai aka isar da shi dandalin gaisuwa domin karrama shi ta hanyar jiniya da sara masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel