Daga Zuwa Yawon Kamfe, Kwankwaso Ya Samu Sarautar Gargajiya na 'Jarumin Karshi'

Daga Zuwa Yawon Kamfe, Kwankwaso Ya Samu Sarautar Gargajiya na 'Jarumin Karshi'

  • Sarkin Karshi ya karbi bakuncin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da kyau yayin da ya ziyarci fadarsa
  • Kamar yadda ya saba, idan ya je kamfe a gari, ‘Dan takaran NNPP ya kan ziyarci Sarakuna da ke mulki
  • Muhammad Sani Bako III ya ba Kwankwaso sarautar Jarumin Karshi da ya je mika gaisuwa a ranar Litinin

A ranar Litinin, 16 ga watan Junairu 2023, Rabiu Musa Kwankwaso da mutanensa suka ziyarci Sarkin Karshi watau Alhaji (Dr) Muhammad Sani Bako III.

‘Dan takaran kujerar shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso da ‘yan tawagarsa sun je yawon yakin zabe ne a jihar Nasarawa.

A farkon makon nan jam’iyyar NNPP ta gudanar da babban taron yakin neman zabenta na jihohin Arewa maso tsakiya, an shirya taron ne a birnin Lafia.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya kada hantar su Atiku da Tinubu, dubban mutane sun tarbe shi a wata jihar Arewa

Bayan wannan gangami sai Rabiu Kwankwaso ya kai ziyara zuwa fadar Mai martaba Sarkin Karshi a Nasarawa domin ya mika gaisuwar ban-girma.

Jarumin Karshi

A wajen ne aka ji cewa Mai martaba ya ba Kwankwaso sarautar gargajiyar Jarumin Karshi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon Gwamnan na jihar Kano ya bayyana haka a shafinsa na Twitter a yammacin Litinin, inda aka ji ya yi wa Sarkin na Karshi godiya ta musamman.

Rabiu Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso a Karshi Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

“Ina mai mika cikakkiyar godiya da jinjina ga Mai martaba Sarkin Kashi, Alh. (Dr) Muhammad Sani Bako III, wanda ya ba ni sarautar gargajiyar Jarumin Karshi, a lokacin da muka ziyarci fadarsa a yau.
Nagode, Allah ya kara wa Sarki lafiya.
– Rabiu Musa Kwankwaso

Wannan ne karo na farko da Legit.ng Hausa ta samu labarin an ba Sanata Kwankwaso sarauta.

Kwankwaso da gidan sarauta

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Yi Gini a Kan Ruwa, Jagoran Kamfe da Mutanensa Sun Watse Daga NNPP

‘Dan siyasar ya tashi ne a gidan sarauta domin mahaifinsa ya yi shekara da shekaru yana rike da sarautar Hakimin Madobi kuma Majidadin kasar Kano.

Daga baya da gwamnatin jihar Kano ta raba masarautu, Madobi ta koma karkashin masarautar Karaye, ya cigaba da rike sarautar Makaman Karaye.

A duk shekarun nan, Kwankwaso bai taba samun sarauta a Kano ko a ji yana tsoma baki a kan lamarin ba, yanzu kaninsa ne yake Hakimi a Madobi.

NNPP tayi rashi

Dazu an ji labari cewa anda Rabiu Musa Kwankwaso ya dogara da shi a Arewa maso gabas, ya fice daga jam’iyyar NNPP, ya kuma sauya-sheka zuwa PDP.

Dr. Babayo Liman ya ajiye mukamin Sakatare a jam'iyyar NNPP da jagorancin Kwankwasiyya, ya fadawa magoya bayansa su zabi Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel